Sharhi: Dalilin Kirkirar Rundunonin Tsaro a Jihohin da ke Fama da Ƴan Bindiga a Arewa

Sharhi: Dalilin Kirkirar Rundunonin Tsaro a Jihohin da ke Fama da Ƴan Bindiga a Arewa

  • Jihohin gwamnonin Arewacin Najeriya musamman na yankin Arewa maso Yamma na fama da matsalar rashin tsaro
  • A jihohin dai ƴan bindiga da ƴan ta'adda na cin karensu babu babbaka inda suka hana mutane zama cikin kwanciyar hankali
  • Domin magance matsalar, wasu gwamnonin jihohin yankin sun kafa rundunar tsaro domin kawo ƙarshen ayyukan miyagun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Matsalar rashin tsaro ta daɗe tana addabar yankin Arewacin Najeriya, musamman jihohin da ke yankin Arewa maso Yamma.

Jihohin Katsina, Kaduna, Kebbi, Sokoto da Zamfara sun kasance suna fuskantar hare-haren ƴan bindiga da ƴan ta'adda waɗanda ke cin karensu babu babbaka.

Dalilin samar da rundunar tsaro a Arewa
Gwamnonin Katsina, Zamfara da Sokoto sun kafa rundunar tsaro Hoto: Dauda Lawal, Dr. Dikko Umaru Radda, Ahmed Aliyu
Asali: Facebook

Hare-haren na ƴan bindigan da satar mutane domin biyan kuɗaɗen fansa ya jawo asarar rayuka masu ɗumbin yawa da dukiyoyi. Mutane da dama sun rasa matsugunansu inda suka koma ƴan gudun hijira a wasu garuruwan

Kara karanta wannan

Sace-sace a Kaduna da Borno: An ba Shugaba Tinubu mafita

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani rahoto da International Review of Red Cross ta fitar, ta ce ƴan bindiga sun halaka mutum 6319, sun sace mutum 3762 da ƙona ƙauyuka 500 a jihar Zamfara daga shekarar 2011 zuwa 2019.

Rahoton ya kuma ce ƴan bindigan sun farmaki makarantu 20 inda suka sace ɗalibai aƙalla 1436 a yankin Arewa maso Yamma a shekarar 2021.

Wane ƙoƙari gwamnatoci ke yi a Arewa?

A baya wasu daga cikin gwamnonin jihohin sun bi hanyar yin sulhu da ƴan bindigan domin kawo ƙarshen matsalar.

A jihar Katsina, gwamnan da ya gabata, Aminu Bello Masari, ya yi sulhu da ƴan bindiga domin su ajiye makamansu su rungumi zaman lafiya.

Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma ƙaramin ministan tsaro a yanzu, Bello Matawalle, shi ma ya bi wannan hanyar ta tattaunawa da ƴan bindiga.

Sai dai, wannan hanyar da suka bi bata ɓulle ba, domin hakan bai sanya an kawo ƙarshen matsalar ba, hasalima sai ƙara ta'azzara da ta yi.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun faɗi malamin Musulunci 1 da suke goyon bayan ya tattauna da ƴan bindiga

An ɗauki sabon salo

A ƙoƙarin shawo kan matsalar rashin tsaron, wasu daga cikin gwamnonin jihohin yankin Arewa maso Yamma, sun ɗauki sabon salo domin kawo ƙarshen matsalar.

Wasu daga cikin gwamnonin sun ɗauki matakin samar da rundunar sa-kai da za ta taimakawa jami'an tsaro wajen gudanar da ayyukansu.

Jihohin da suka kafa rundunar tsaro

A ranar 10 ga watan Oktoban 2023, gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ƙaddamar da rundunar tsaro ta 'Katsina Community Watch Corps' domin kawo ƙsrshen ƴan bindiga.

Jami'an rundunar ta KCWC sun samu cikakken horo tare kayan aiki waɗanɗa za su taimaka musu wajen yaƙi da miyagun.

Bayan jihar Katsina, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, shi ma ya bi sahu wajen ƙaddamar da rundunar tsaron da za ta yi fito na fito da ƴan bindiga.

Rundunar tsaron wace aka sanya suna 'Askawaran Zamfara' na da jami'ai mutum 2,645 waɗanda za su taimakawa jami'an tsaro kawo ƙarshen ƴan bindiga.

Kara karanta wannan

Ana cikin azumi 'yan ta'adda sun kai mummunan hari a jihar Arewa

A ranar Asabar, 9 ga watan Maris, 2024, jihar Sokoto ta zama jiha ta uku a yankin Arewa maso Yadda wajen ƙaddamar da rundunar tsaronta wacce za ta yi fito na fito da miyagun ƴan bindiga..

Meyasa aka kafa sabuwar rundunar tsaro

Gwamnonin dai sun kafa rundunar tsaron ne da nufin daƙile matsalar rashin tsaro da ta addabi yankin na tsawon shekara da shekaru.

Rundunonin tsaron za su riƙa taimakawa jami'an tsaro wajen gudanar da ayyukansu a yaƙin da suke yi da ƴan bindiga.

An dai kafa rundunar tsaron ne da fatan cewa matsalar rashin tsaro da addabi yankin za ta zama tarihi, sannan a samu zaman lafiya mai ɗorewa.

Matsalolin da ƴan banga za su fuskanta

1. Ba su da ikon rike manyan makamai

2. Dokar kasa ba ta ba jihohi ikon kafa ‘yan sanda ba

3. Ana zarginsu da keta hakkin al’umma wajen aiki

Rashin tsaro: Mafita ga gwamnonin Arewa

Kara karanta wannan

Shugabannin APC sun faɗawa Tinubu mataki 1 da ya kamata ya ɗauka kan wasu hafsoshin tsaro a Najeriya

1. Ƙarfafa jami’an sa-kai da ƴan banga a doka

2. Ƙirƙiro da ƴan sandan jihohi a kundin tsarin mulki

3. Ƴan banga su haɗa-kai da sojoji da ƴan sandan ƙasa

Abubuwan sani dangane da rundunar KCWC

A baya rahoto ya zo kan muhimman abubuwan da ya kamata ku sani dangane da rundunar tsaro ta KCWC da aka kafa a jihar Katsina.

Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda, shi ne ya ƙaddamar da rundunar wacce za ta yi fito na fito da ƴan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng