Buga Takardun Bogi: Kotu Ta Dauki Mataki Kan Tsohon Shugaban Bankin NIRSAL, Abdulhameed
- Rundunar 'yan sanda ta gurfanar da tsohon shugaban bankin NIRSAL, Aliyu Abdulhameed a gaban kotun tarayya da ke Abuja
- An gurfanar da Abdulhameed ne bisa zarginsa da aikata laifuffuka 10 da suka shafi hada baki don aikata laifi da kuma buga takardun bogi
- Mai Shari'a Inyang Ekwo, ya fara yanke hukuncin farko kan shari'ar bayan sauraron bangaren mai kara da wadanda ake karar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - A ranar Laraba, rundunar 'yan sanda ta gurfanar da tsohon shugaban (MD) bankin lamunin noma NIRSAL, Aliyu Abdulhameed a gaban kotun tarayya da ke Abuja.
Jaridar Legit Hausa, a ranar 1 ga watan Disamba, 2022 ta ruwaito cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsige Abdulhameed daga mukaminsa.
An gurfanar da tsohon shugaban NIRSAL din ne tare da wani Babangida Abdullahi bisa zargin su da aikata laifuka 10 da suka shafi hada baki da buga takardun bogi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar 'yan sandan ta shaida wa kotun cewa wadanda ake kara sun aikata laifin buga takardun bogi a ranar 23 ga watan Oktoba, 2023.
"Ina da kwararan hujjoji" - Odo
Jaridar Tribune Online ta ruwaito cewa wadanda ake karar, sun musanta aikata wadannan tuhume-tuhume bayan an karanta masu.
Jami'i mai shigar da kara, Celestine Odo, ya bukaci kotun da ta bayar da ajiyar wadanda ake karar a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja.
Odo ya kuma shaida wa kotun cewa yana da kwararan hujjoji da kuma mutane biyar da za su ba da shaida domin tabbatar da laifuffukan da ake zargin mutanen biyu sun aikata.
An nemi belin Abdulhameed
Rahoton Vanguard, ya nuna cewa lauyan wadanda ake kara, Akin Olujimi (SAN), ya nemi belin wadanda yake karewa.
Ko da alkalin kotun, Mai shari'a Inyang Ekwo ya tambayi mai shigar da karar ko yana da ja kan hakan, Odo ya ce ba zai yi jayayya da bukatar neman belin ba.
Mai Shari'a Ekwo ya bukaci lauyan wadanda ake karar da ya tattara takardun bukatar belin ya mika wa magatakardar kotun, tare da dage shari'ar zuwa ranakun 20, 21, 22 da 23 ga watan Mayu domin fara sauraron karar.
Kotu ta kwace N1.5b daga hannun Abdulhameed
A baya Legit Hausa ta ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya da ke da zama a Abuja, ta kwace Naira biliyan 1.5 daga hannun Aliyu Abdulhameed.
Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Abdulhameed, tsohon shugaban bankin NIRSAL a gaban Mai shari'a Inyang Ekwo, bisa zargin ya aikata barna a lokacin da ya ke kan kujerarsa.
Asali: Legit.ng