Sanata Yari Zai Hada Kai da Atiku Domin Kafa Sabuwar Jam’iyya? Gaskiya Ta Bayyana
- Sanata Abdulaziz Yari daga Zamfara ta Yamma ya karyata rahoton cewa yana da hannu a shirin Atiku na kafa sabuwar jam'iyya
- Wani rahoto ya nuna cewa Atiku yana so ya kafa sabuwar jam'iyya ne domin kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2027
- Sai dai, tawagar yada labarai ta Sanata Yari, ta ce babu hannun sanatan a wannan shiri kuma har gobe yana tare da APC da Shugaba Tinubu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Sanata Abdulaziz Yari daga Zamfara ta Yamma ya karyata rahoton da ke yawo na cewa ya hada kai da Atiku Abubakar domin kafa sabuwar jam’iyyar siyasa.
Rahotannin sun ce ya hada kai da Abubakar, da kuma Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya, Abdul Ningi da aka dakatar a halin yanzu don kafa jam'iyyar.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Atiku yana so ya kafa sabuwar jam'iyyar a matsayin wani shiri na kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai Atiku ya musanta wannan zargin, inda ya bayyana cewa ya mayar da hankali ne kawai wajen samar da hadin kai a tsakanin jam’iyyun adawa.
Babu hannun Yari a 'shirin' Atiku
Tawagar Yari ta kafafen yada labarai ta sanar a ranar Laraba cewa tsohon gwamnan Zamfara fitaccen mutum ne a cikin jam’iyyar APC kuma yana tafiya ne kan manufofinta.
A cikin sanarwar da jaridar The Cable ta samu, tawagar Yari ta kafafen yada labarai ta ce:
“Ofishin yada labarai na mai girma Sanata Abdulaziz Yari, ya musanta rade-radin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa na cewa Sanata Yari na da hannu wajen kafa sabuwar jam’iyyar siyasa.
“Sanata Yari, a matsayinsa na jagoran jam’iyyar APC a Zamfara, ya jajirce wajen ganin jam’iyyar ta cimma burinta na Nijeriya."
Yari na tare da Tinubu ko Atiku?
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
“A matsayinsa na dan majalisa, Sanata Yari ya yi aiki kafada-da-kafada da takwarorinsa a majalisar dattawa ta 10 domin karfafa manufar jam’iyyar a majalisar dokokin kasa.
"Sanata Yari ya himmatu wajen yin aiki tare da jam'iyyar APC da kuma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin inganta rayuwar 'yan Najeriya baki daya."
Yari zai tallafawa mutane miliyan 1.25
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa, Sanata Abdul'aziz Yari, ya kaddamar da rabon kayan abinci ga mutane miliyan 1.25 kamar yadda ya saba a kowanne watan azumi.
Shugaban kwamitin rabon kayan, Lawal M. Liman ya bayyana cewa za a yi rabon ne ba tare da la'akari da bambancin siyasa ba, tare da fatan wadanda suka cancanta ne za su samu.
Asali: Legit.ng