Hukumar Hisbah Ta Kama Musulman da Ke Cin Abinci a Bainar Jama’a Ana Azumi
- Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama wasu Musulmai 11 da ke cin abinci a bainar jama'a a lokacin azumin watan Ramadan
- Hisbah ta kama mutanen ne bayan da ta gudanar da bincike a gidajen cin abinci da kasuwanni kamar yadda ta saba yi duk shekara
- Kafin hukumar ta sake su, wadanda aka kaman, maza 10 da mace daya, sun yi rantsuwa kan cewa ba za su sake aikata hakan ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Hukumar Hisbah a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta kama wasu musulmi 11 a ranar Talata wadanda aka gansu suna cin abinci da rana a lokacin azumin watan Ramadan.
Musulmi su ne mafi rinjaye a al'ummar jihar Kano kuma jihar na bin tsarin shari'ar Musulunci sau da kafa wanda hakan ne ma ta sa aka kama mutanen.

Kara karanta wannan
Azumin Ramadan: Hisbah ta aika da muhimmin gargadi ga wadanda ba musulmai ba a Kano

Asali: Facebook
Hisbah ta kama mutanen ne bayan da ta gudanar da bincike a gidajen cin abinci da kasuwanni kamar yadda ta saba yi duk shekara a cikin watan Ramadan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa hukumar ta saki mutanen 11 (maza 10 da mace daya) bayan sun yi rantsuwa cewa ba za su sake cin abinci a bainar jama'a alhalin ana yin azumi ba.
Za a kama wadanda ba Musulmai ba?
Kakakin hukumar Hisbah na Kano, Lawal Fagge ya shaida wa BBC cewa:
"Mun kama mutane 11 a ranar Talata ciki har da wata budurwa mai sayar da gyada da aka ga tana cin gyadar a bainar jama'a, wasu mutane suka kai mana rahoto."
“Sauran 10 din maza ne kuma an kama su a sassa daban-daban na birnin jihar musamman kusa da kasuwannin da ake yawan hada-hada."
Ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da bincike amma ya ce an kebe wadanda ba musulmi ba daga wadanda za a kama.
"Zamu kama wadanda ba musulmi ba ne kawai idan muka gano cewa suna dafa abinci don sayar wa musulmi da ya kamata a ce suna yin azumi."
- A cewar Lawal Fagge.
Hisbah ta gargadi wadanda ba Musulmi ba
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa, hukumar Hisbah ta Kano ta gargadi wadanda ba Musuli ba a jihar da kada su rinka cin abinci a fili ko kuma su yi wani abu da zai gurgunta addinin Musulunci.
Darakta Janar na hukumar, Abba Sai’Idu ya ce jami'an hukumar za su tsaurara sintiri a cikin gari domin kame duk wani musulmi da aka gani yana aikata wani aiki da bai dace da al’adar Musulunci ba.
Asali: Legit.ng