Yayin da Ake Cikin Wani Hali, Tinubu Ya Bada Umarnin Bude Iyakokin Najeriya, Bayani Sun Fito
- Yayin da ake da kiraye-kiraye ga Bola Tinubu kan bude iyakoki, da alamu ya ji korafin jama'ar Najeriya
- Shugaban ya bayar da umarni bude iyakokin sama da kuma na tudu da ke tsakanin Najeriya da Nijar
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayar da umarnin bude iyakokin da ke tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Umarnin zai shafi dukkan iyakokin da ke kan tudu da kuma sama tare da dage duk wasu takunkumai da aka kakaba wa kasar a kwanakin baya.
Wane umarni Tinubu ya bayar kan iyakoki?
Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya sanar da haka a yau Laraba 13 ga watan Maris a birnin Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, Ngelale ya ce wannan mataki ya biyo bayan shawarar da Shugabannin Kungiyar ECOWAS suka yanke a taron da suka gudanar na a ranar 24 ga watan Fabrairu.
Wannan na zuwa ne yayin da 'yan kasar ke kiraye-kirayen bude iyakokin kasar gaba daya domin samun sauƙin shigowa da kayayyaki daban-daban.
Takunkuman da aka ƙaƙabawa Nijar a baya
Daga cikin matakan da Tinubu ya dauka a baya akwai rufe iyakokin sama da ƙasa tsakanin Najeriya da Nijar.
Har ila yau, ya kuma hana zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci wanda ECOWAS ta saka.
Sauran sun hada da dakatar da dukkan cinikayya tsakanin Najeriya da Nijar da dakatar da ba Nijar wutar lantarki.
Sannan akwai dakatar da ba Nijar duk wani tallafi na kuɗi da daina cinikayya da haramta tafiye-tafiye ga jami’an gwamnati da iyalansu.
Kwastam ta magantu kan bude iyakoki
Kun ji cewa Hukumar Kwastam ta yi magana kan shirye-shiryen Shugaba Tinubu game da bude iyakokin Najeriya.
Hukumar ta sanar da cewa Shugaba Tinubu ne kadai yake da ikon bude iyakokin Najeriya bisa tsarin doka.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ta kiraye-kirayen a bude iyakokin kasar ko za a samu sauki a halin kunci da ake ciki.
Asali: Legit.ng