Yayin da Ake Azumi Babu Wuta, Ministan Tinubu Ya Yi Magana Kan Tallafin Lantarki, Ya Yi Gargadi
- Ministan makamashi ya yi magana kan tallafin man fetur a Najeriya da kuma matsalar da ake samu kan samar da wutar lantarki
- Adebayo Adelabu ya gargadi kamfanonin samar da wutar kan inganta lantarki inda ya ce za su dauki mataki mai tsauri kan lamarin
- Ministan ya ce za a ci gaba da biyan kudin tallafin wutar zuwa wani lokacin yayin da za a rinka janye shi a hankali har karshe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Yayin da ake fama da karancin wutar lantarki, Ministan makamashi ya yi magana kan inganta wutar lantarki a Najeriya.
Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce za su dauki mataki kan kamfanonin samar da wutar na DISCO da GENCOS kan matsalar da ake samu game da wutar lantarki.
Gargadin Adelabu kan matsalar wutar lantarki
Adelabu ya gargade su kan rashin ba da wutar inda ya ce za su kwace lasisin kamfanonin da ke kokarin kawo cikas a inganta wutar, cewar NTA News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce za a ci gaba da biyan kudin tallafin wutar kafin janyewa a hankali har zuwa lokacin da za a janye gaba daya.
“Muna da tsarin da muka yi a ajiye, wannan zai shafi dukkan kudin haraji da kuma kudin tallafin wutar a Najeriya.”
“Za a ci gaba da biyan tallafin wutar amma za a rika cirewa a hankali har zuwa lokacin da za a cire tallafin gaba daya.”
- Adebayo Adelabu
Har ila yau, ya koka kan yadda cikin makwanni biyu samar da wutar ya yi karanci a fadin kasar duk da biyan tallafi har kaso 65 na tallafi.
Shirin cire tallafin wutar lantarki
Wannan na zuwa ne yayin da ake hasashen gwamnatin ta shirya cire tallafin wutar lantarki duk da halin kunci da ake ciki.
Gwamnatin Tarayya ta bakin Minista Adelabu ta sanar da cewa ba za ta iya ci gaba da biyan kudaden tallafi ba.
Ministan ya bayyana cewa tarun bakusan da kamfanonin ke bin gwamnati ya yi yawa duk da kokarin biyan da ake yi.
Lantarki: Majalisa ta nuna fushinta
Kun ji cewa Majalisar Tarayya ta nuna damuwa kan yadda ake kokarin cire tallafin wutar lantarki a Najeriya.
Wannan na zuwa ne yayin da ‘yan kasar ke cikin mawuyacin hali bayan cire tallafin man fetur a kasar.
Asali: Legit.ng