An Hargitse a Majalisa Kan Zargin Sanata Ningi, an Fifita Manyan Sanatoci Wurin Rabon Kudi

An Hargitse a Majalisa Kan Zargin Sanata Ningi, an Fifita Manyan Sanatoci Wurin Rabon Kudi

  • Yayin Sanata Abdul Ningi yake zargin cushe a kasafin kudin shekarar 2024, Majalisa ta rikice a yanzu haka kan lamarin
  • Idan ba a manta ba Ningi ya yi zargin cewa an yi wa Najeriya illa sosai a kasafin da aka gabatar na wannan shekara a Majalisar
  • Wannan zargi na sanatan daga jihar Bauchi ya jawo rudani da kace-nace kan lamarin inda wasu ke neman a hukunta shi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ana cikin dambarwa yanzu haka a Majalisar Dattawa kan zargin cushe a kasafin kudin shekarar 2024.

Wannan cece-kuce a Majalisar na zuwa ne bayan Sanata Solomon Olamilekan Ademola ya gabatar da kudirin kan matsalar, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Yayin da ake azumi babu wuta, Ministan Tinubu ya yi magana kan tallafin lantarki, ya yi gargadi

An shiga hargitsi a Majalisa kan zargin nuna wariya a rabon kudi
Lamarin ya faru ne kan zargin cushe a kasafin kudin shekarar 2024. Hoto: The Nigerian Senate.
Asali: Facebook

Menene ya jawo cece-kuce a Majalisar?

A karshen makon jiya ne Sanata Abdul Ningi daga jihar Bauchi ya tada ƙura inda ya ce akwai matsala a kasafin kudin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ningi ya tabbatar da cewa an yi wa Najeriya mummunan illa a cikin kasafin kudin da aka gabatar a gaban Majalisar tarayya.

Adeola ya ce an ci mutuncinsa lokacin da ya shiga gabatar da kasafin kudin a Majalisar.

"Ningi ya yi zargin cewa akwai biliyan uku wadanda babu abin da za a yi da su a cikin kasafin kudin."

- Solomon Adeola

Zargin nuna wariya kan rabon kudi

Majalisar ta sake hargitsewa bayan da wani Sanata Jarigbe Jarigbe daga Kuros Riba ya yi zargin wasu manyan sanatoci sun samu miliyan 500 a matsayin kudin ayyuka a yankunansu.

"Idan har zan bude komai a wannan matsalar, wasu daga cikin manyan sanatoci sun samu fiye da miliyan 500 amma ni a matsayin sanata ko sisin kwabo ban samu ba."

Kara karanta wannan

Kotu ta dauki tsattsauran hukunci kan likitan bogi da ake zargin ya kashe majinyaci

"Shin ya kamata na fadawa 'yan jaridu?"

-Sanata Jarigbe

An dakatar da Sanata Ningi

Kun ji cewa Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Abdul Ningi bisa zargin da ya yi na yin cushe a kasafin kuɗi na 2024.

An dakatar da Ningi wanda ke wakiltar Bauchi ta tsakiya na tsawon watanni uku bayan wata doguwar mahawarar da aka yi a zauren Majalisar.

Wannan na zuwa ne bayan zargin da sanatan ya yi kan an yi wa Najeriya illa a kasafin kudin shekarar 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.