Gwamnan APC ya amince zai raba tallafin abinci ga talakawa sama da miliyan 2 a Ramadan
- Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya kaddamar da kwamitin da zai jagoranci ciyar da talakawa marasa galihu sama da miliyan biyu a Katsina
- Gwamnan ya bayyana cewa shirin zai tallafawa kimanin mutane 72,000 a kowace rana tun daga farkon watan Ramadan zuwa karshe
- A yau Litinin, Musulman Najeriya da wasu ƙasashen duniya suka fara azumin watan Ramadan bayan sanarwan ganin jinjirin wata
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin Malam Dikko Raɗda ta shirya ciyar da mutane 2,166,000 masu ƙaramin karfi a tsawon kwanakin watan Ramadan.
Gwamnan jihar, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ne ya bayyana haka a wurin kaddamar da kwamitin da zai jagoranci raba tallafin a matakin jiha da ƙananan hukumomi.
Ranar Litinin, 11 ga watan Maris, 2024, Musulmai a Najeriya da wasu sassan duniya suka tashi da azumin watan Ramadan bayan ganin jinjirin wata ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda gwamnatin Katsina ta tsara tallafin Ramadan
A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren watsa labaransa, Ibrahim Kaula Muhammed, Gwamna Radda ya ce shirin zai ciyar da talakawa 72,200 kowace rana.
A rahoton Leadership, sanarwar ta ce:
"Shirin ya tsara yadda za a ciyar da kimanin mutane 72,200 a kowace rana a Ramadan, wanda idan aka haɗa jimulla mutane kusan 2,166,000 zasu amfana da tallafin abinci a tsawon watan.
"Kamar yadda Gwamna Radda ya sanar, shirin ya ƙunshi rage farashin masara, gero da dawa zuwa N20,000 kan kowane buhu ɗaya.
"Bayan rage farashin kayan abinci ga magidanta 400,000, gwamnan ya ce za a raba kayan abinci kyauta ga tsofaffi da iyalai marasa galihu 33,000 a sassan jihar Katsina."
Ya kara da cewa gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar kananan hukumomi 34 sun ware sama da Naira biliyan 10 wajen siyan hatsi domin rabawa talakawan Katsina.
Raɗɗa ya nada Mallam Khalil Musa Kofar Bai a matsayin shugaban kwamitin, sauran mambobin kwamitin sun hada da wakilan yankuna da kungiyoyi daban-daban, rahoton This Day.
Mazauna Katsina sun shaidawa Legit Hausa cewa wannan abu ne mai kyau amma fatansu Allah ya sa tallafin ya isa ga waɗanda aka yi dominsu.
Yahuza Abdullahi, malamin makaranta a ƙaramar hukumar hukumar Ɗanja, ya ce wannan abu ne mai kyau a watan Ramadan amma abin dubawan shi ne su wa zasu ci tallafin.
"Ramadan wata ne na ciyarwa da taimaka wa gajiyayyu, muna fatan Allah ya sa saƙon ya isa ga waɗanda ake so a taimaka, domin wani lokacin siyasa ake sa wa."
Faisal Ahmad ya ce a ganinsa ba wannan al'umma suke buƙata ba a halin tsadar da ake ciki.
Ya faɗawa wakilin mu cewa, "Bana tunanin wannan mafita ce, yanzu an ce za a bada tallafi sai kaga ana rabawa mutane shinkafa tiya ɗaya, abincin rana ɗaya.
"Daga nan shikenan ba mai ƙara waiwayenka, a ganina abinci ya yi arha yadda mai ƙaramin karfi zai iya sa kuɗinsa ya siya."
Ramadan: IGP jadadda kudirin samar da tsaro
A wani rahoton Rundunar ƴan sanda ta aike da saƙon gaisuwa da taya murna ga Musulmin Najeriya yayin da suka fara azumtar watan Ramadan.
Sufetan ƴan sandan na kasa ya jaddada shirin rundunar na tabbatar da tsaro a lungu da saƙon Najeriya a wannan wata mai albarka.
Asali: Legit.ng