Shugaba Bola Tinubu Ya Samu Karramawa Ta Musamman a Jihar Neja

Shugaba Bola Tinubu Ya Samu Karramawa Ta Musamman a Jihar Neja

  • Gwamnatin jihar Neja ta sanar da cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu zai kai ziyara jihar a yau Litinin, 11 ga watan Maris, 2024
  • Gwamnatin ta tabbatar da cewa an kammala dukkan shirye-shirye domin tarbar shugaban ƙasan
  • Bugu da ƙari, Gwamna Bago na jihar ya sauya sunan filin jirgin saman Minna, wanda a baya aka sanyawa sunan Abubakar Iman, zuwa na Shugaba Tinubu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Minna, jihar Neja - Umar Bago, gwamnan jihar Neja, ya yanke shawarar sauya sunan filin jirgin saman Abubakar Imam da ke Minna domin karrama shugaban ƙasa Bola Tinubu.

A ranar Litinin, 11 ga watan Maris, 2024. Tinubu zai kai ziyara Minna, babban birnin jihar, domin ƙaddamar da wasu muhimman ayyukan da gwamnatin jihar ta yi.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya yi sa'insa da Akpabio a wurin jana'izar Herbert Wigwe, bidiyo ya bayyana

An sanya wa tashar jirgin saman Minna sunan Tinubu
Tashar jirgin saman Minna ta samu sunan Shugaba Tinubu Hoto: @DeeOneAyekotoo
Asali: Twitter

Aminu Takuma kwamishinan masana’antu, kasuwanci da zuba jari, shi ne ya bayyana hakan ta bakin wakilinsa, Isah Adamu, a yayin ganawa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar dake Minna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka sanyawa tashar sunan Shugaba Tinubu?

Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, Takuma ya bayyana cewa goyon bayan da shugaban ƙasan ya ba jihar ne ya sa aka yanke shawarar sauya sunan filin jirgin saman zuwa sunansa.

Ya ƙara da cewa, Tinubu zai kuma halarci bikin ƙaddamar da ɓangaren tashin Alhazai a filin jirgin saman.

Tinubu zai ƙaddamar da kayan ayyukan noma a Neja

Haka zalika, gidan talabijin na Channels tv ya ruwaito cewa, Shugaba Tinubu zai ƙaddamar da kayayyakin noma na biliyoyin kudi da gwamnatin jihar ta samar.

A cewar kwamishiniyar yaɗa labarai da dabarun jihar, Hon. Binta Mamman, an kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace don ganin komai ya tafi daidai a yayin ziyarar shugaban ƙasan.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya maida zazzafan martani kan garkuwa da ɗalibai da ƴan gudun hijira a jihohi 2

Shugaba Tinubu ya shawarci masu abun hannnu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga masu hannu da shuni da za su taimakawa marasa galihu musamman a lokacin watan Ramadan.

Shugaban ƙasan ya yi wannan kiran ne yayin da al'ummar musumai suka fara azumin watan Ramadan na shekarar 1445 bayan hijira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng