Gwamnatin Tinubu Na Amfani da Kasafin Kudi Iri 2 a 2024? Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Gaskiya

Gwamnatin Tinubu Na Amfani da Kasafin Kudi Iri 2 a 2024? Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Gaskiya

  • Fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani kan iƙirarin da Sanata Abdul Ningi ya yi cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu na gudanar da kasafin kuɗin 2024 iri biyu
  • Sanata Ningi, a ƙarƙashin ƙungiyar Sanatocin Arewa, ya yi iƙirarin cewa majalisar ta tattauna tare da amincewa da kasafin kuɗin shekarar 2024 na Naira Tiriliyan 25, maimakon Naira Tiriliyan 28.7
  • A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 10 ga watan Maris, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana iƙirarin a matsayin ƙarya da yaudara

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Fadar shugaban ƙasan Najeriya ta ce iƙirarin da Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta tsakiya ya yi na cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu na gudanar da kasafin kuɗin 2024 guda biyu, ƙarya ce.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Kabir ya yi muhimmin gyara a babbar kotun Kano da kotun shari'ar musulunci

A cewar wata sanarwa a yammacin ranar Lahadi, 10 ga watan Maris, mai taken 'tabbatattun bayanai game da kasafin kuɗin 2024', daga Bayo Onanuga, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa Tinubu kan yada labarai da dabaru, Sanata Ningi kawai surutu yake yi.

Fadar shugaban kasa ta yi martani ga Sanata Ningi
Fadar shugaban kasa ta musanta batun amfani da kasafin kudi iri biyu na 2024 Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Me fadar ta ce kan zargin Sanata Ningi?

Fadar shugaban ƙasan ta kuma caccaki Sanata Ningi kan iƙirarin da ya yi na cewa kasafin kuɗin 2024 ya bar yankin Arewa a baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta yi nuni da cewa Shugaba Tinubu yana jagorantar gwamnati mai adalci ga kowane ɓangare na Najeriya.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Shugaba Tinubu mai cikakken imani ne kan bin doka da oda da tsarin mulkin dimokuradiyya. A matsayinsa na mai fafutukar tabbatar da dimokuradiyya, ba zai tsunduma wajen aiwatar da duk wani mataki da ya saɓa wa kundin tsarin mulki ba, ko kuma yin duk wani abu da ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya, ta hanyar gudanar da wani kasafin kuɗi wanda ba majalisar tarayya ta amince da shi ba, wanda ya rattaɓa wa hannu bisa bin doka da oda.

Kara karanta wannan

Ana ba tsaro a kasa, Akpabio ya fito ya fadi ci gaban da Tinubu ya kawo a bangaren

"Muna so mu bayyana dalla-dalla cewa kasafin kuɗin 2024 ɗaya tilo da ake aiwatarwa shi ne kasafin Naira Tiriliyan 28.7 da majalisar tarayya ta amince da shi kuma shugaban ƙasa ya sanya wa hannu."

- Bayo Onanuga

Gwamnatin tarayya da jihohi sun samu kudade daga FAAC

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya, jihohi 36 da ƙananan hukumomi sun samu N1.1trn a watan Janairun 2024 daga asusun FAAC.

Asusun wanda ke da alhakin raba kuɗaɗen shigar da aka samu, ya bayar da kuɗaɗen ne domin ɓangororin na gwamnati su gudanar da ayyukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng