“Akwai Fa’idodi a Zaman Najeriya”: Budurwa Da Ke Zaune a Turai Ta Fadi Wahalhalun da Suke Sha

“Akwai Fa’idodi a Zaman Najeriya”: Budurwa Da Ke Zaune a Turai Ta Fadi Wahalhalun da Suke Sha

  • Wata matashiyar budurwa a turai ta ce akwai wasu illoli da ke tattare da tafiya kasashen waje da zama a can
  • A cewarta, mutane da ke zaune a Najeriya suna more wasu abubuwa da takwarorinsu na turai basa morewa
  • Ta ce yayin da mutum ke iya yin fitsari a duk inda yake so a Najeriya, irin hakan ba mai yiwuwa bane a kasar da take da zama

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wata matashiya ta lissafa wasu fa'idodi da alfanun da ke tattare da zaman Najeriya maimakon turai.

Matashiyar ta wallafa bidiyon a shafinta na TikTok, @rca228, sannan ta bayyana cewa akwai alfanu sosai a zaman Najeriya.

Matashiya ta ce Najeriya ta fi turai dadin zama
Matashiyar ta ce mutum na iya yin fitsari a waje a Najeriya Hoto: TikTok@rca228 da Getty Images/Aaron Foster
Asali: UGC

A cewarta, yayin da mutanen da ke zaune a Najeriya za su iya more wasu abubuwa, kamar su fitsari a waje, wadanda ke turai ba za su iya ba.

Kara karanta wannan

Budurwa ta siya katon gida a turai tana da shekaru 22, ta yi murnar zama mai gidan kanta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta jaddada cewar wadanda ke Najeriya za su iya gaggauta shiga daji don yin bahaya, amma hakan ba mai yiwuwa bane a turai.

Saboda haka, ta fada ma mutanen da ke zaune a Najeriya da su ji dadin damammakin da suke da su wadanda 'yan turai basu da iko a kansu.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@oluebube ya ce:

"Kada ki damu kwannan nan za a koro ki da izinin Allah, kawai ki ce amin."

@chijiokeadinnu ya ce:

"Ki dawo mana idan kin san kin haifu da kyau hajiya."

@BigBee ya ce:

"Toh me yasa kike a UK kenan?"

@YO FaVe BF ya ce:

"Naija ta fi dadi amma babu kudi."

@Tonia ta ce:

"Kana iya hawa babur a gaban gidanka amma a UK sai ka taka zuwa tashar mota."

Kara karanta wannan

"Sun ce ba zan auru ba": Saurayi ya auri matar da ta haifi yara 4, an yi biki na kece raini

@Spareparts_JB ya ce:

"Laifi ne a Najeriya ma, kawai dai ba a aiwatar da dokar yadda ya kamata ne."

'Dan Najeriya ya samu kyautar miliyan 159

A wani labarin, wani 'dan Najeriya ya taki babban sa'a saboda Allah ya tarbawa garinsa nono a lokacin da bai da ko sisi a turai.

Mutumin mai suna Kayode yana a dakin ajiye litattafai yana karatu lokacin da wani mai watsa shirye-shirye a intanet, Zachery Dereniowski ya neme shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel