Yayin da Aka Sanar da Ganin Watan Azumi, Hukumar Tace Fina-finai Ta Dauki Mataki Kan Gidajen Gala
- Yayin da aka shiga cikin wata Ramadana a yau Lahadi 10 ga watan Maris, hukumar tace fina-finai ta dauki wani mataki
- Hukumar ta sanar da rufe dukkan gidajen gala a fadin jihar Kano har sai bayan watan azumi don rage badala a jihar
- Wannan na zuwa ne bayan shugaban hukumar, Abba El-Mustaha a gana da masu gidajen a jihar kan matsalar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Hukumar tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta umarci rufe dukkan gidajen gala a fadin jihar.
Shugaban hukumar a jihar, Abba El-Mustapha shi ya bayyana haka a yau Lahadi 10 ga watan Maris a shafinsa na Facebook.
Wane mataki hukumar tace fina-finai ta dauka?
Abba ya ce an dauki wannan matakin ne saboda shirye-shiryen da ake yi na tukarar watan azumin Ramadan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daukar matakin ya biyo bayan wata ganawa da shugaban hukumar ya yi da jagororin kungiyar masu gidajen gala da ke jihar.
El-Mustapha ya ce dokar za ta fara aiki ne daga yau Lahadi 10 ga watan Maris har zuwa ranar bikin sallah.
Abba El-Mustapha ya tura sakon gargadi
Shugaban hukumar ya gargadi masu gidajen gala da su guji karya doka domin duk wanda ya saba zai fuskanci hukunci mai tasiri.
Ya ce daga cikin matakan da za su dauka shi ne kwace lasisin gidajen galar na din-din-din ga duk wanda ya saba dokar.
Abba ya ce kofarsu a bude take ga duk mai wani korafi ko kuma shawari kan wata matsala da ke faruwa.
Tsohon kwamnadan Hisbah ya magantu kan hukumar
Kun ji cewa tsohon hukumar Hisbah a jihar Kano, Farfesa Ibrahim Muazzam ya bayyana wadanda ke da hannu a yada kamen da hukumar ta yi.
Muazzam ya ce 'yan siyasa ne wadanda basu da wani buri illa kawo cikas a siyasar jihar da kuma cimma burinsu.
Farfesan ya ce abin bai kai yadda aka ta yada shi ba a kafofin sadarwa inda ya ce bukatar 'yan siyasar ba ta biya ba.
Asali: Legit.ng