Gwamnonin Najeriya Sun Magantu Kan Halin Kuncin Da ’Yan Kasa Ke Ciki, Sun Ce Suna Daukar Mataki

Gwamnonin Najeriya Sun Magantu Kan Halin Kuncin Da ’Yan Kasa Ke Ciki, Sun Ce Suna Daukar Mataki

  • Gwamnonin Najeriya na kokarin tabbatar da an warware duk wasu matsalolin tattalin arziki da ake fama dashi a kasar nan
  • AN yi zama tsakanin gwamnoni, sun bayyana abubuwan da suke shirin yi don samar da mafita da wadatuwar abinci nan kusa
  • ‘Yan Najeriya na ci gaba da kuka kan yadda kayan abinci ke kara tsada da kuma yadda kayayyakin ke yankewa a kasuwa kwatsam

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

FCT, Abuja - Gwamnonin jihohi 36 na tarayyar Najeriya sun ce sun bullo da dabaru da daukar matakai daban-daban domin kawo karshen matsalolin tattalin arziki da karancin abinci a jihohinsu.

A cikin wani rahoto mai dauke da sa hannun mukaddashin shugabar sashen yada labarai na kungiyar gwamnoni (NGF), Halimah Salihu Ahmed, ta ce gwamnonin sun dukufa wajen kawo karshen radadin da ‘yan kasa ke ciki.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda da makiyaya ne ke jawo wahalhalun da ake sha a Najeriya, inji fasto Ayodele

Gwamnoni na daukar matakin magance matsalar tattalin arziki
Gwamnoni na magance matsalar tsadar rayuwa | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

Idan baku manta ba, a watan Fabrairu ne shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin jihohin a Abuja, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi tashin farashin kayan masarufi, tabarbarewar tattalin arziki, rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da NGF ta hango, da mafitar da ta kawo

Rahoton na NGF ya bayyana cewa gwamnan jihar Kwara kuma shugaban kungiyar, Abdulrahman Abdulrazaq tare da hadin gwiwar gwamnoni irinsu Agbu Kefas na jihar Taraba; Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo; da kuma Ahmed Ododo na jihar Kogi sun yi ta kokarin ganin an kara habaka fannin noma.

A cewarsu, hakan zai yiwu ne ta hanyar yin amfani da ma’aikatar noma ta kasar, inda za asamar da hanyoyin da za a samu wadataccen abinci, Daily Trust ta ruwaito.

Najeriya dai kasa ce mai yawan girman kasa da jama’a, amma noma ya zama abu mai wahala ga da yawan ‘yan kasar saboda wasu dalilai.

Kara karanta wannan

N11,000/50kg: Hauhawar farashin siminti da matsalolin da yake haifarwa a Najeriya

Matakan da gwamnoni suka dauka a jihohinsu

Hakazalika, rahoton ya bayyana yadda gwamnatoci a jihohin kasar nan suka fara aikin tabbatar da kayan abinci ya sauka don amfanin talakawa.

An buga misali da yadda a baya gwamnatin Kano ta garkame dakunan ajiyar ‘yan kasuwan da ake zargi da Karin farashi ga gaira babu dalili.

Ba Kano ba, jihohi irinsu Yobe, Zamfara, Niger, Ekiti da Legas duk sun dauki matakai don ganin an shawo matsalar.

Abin da ya jawo fatara a kasar nan, inji Fasto

A wani labarin, shugaban cocin INRI, Primate Elijah Ayodele, ya yi ikirarin cewa halin da ake ciki na tabarbarewar tattalin arziki a Najeriya ba komai bane face sakamakon ayyukan kashe-kashe da ‘yan ta’adda da makiyaya ke yi.

Primate Ayodele wanda ya yi magana a ranar Alhamis ya ce idan Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin, to dole tattalin arzikin zai farfado.

Ya sanar da cewa, ya kamata a fara daukar matakai irin wadannan don tabbatar da an hukunta masu tada zaune tsaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.