An Shiga Jimami Yayin da Gwamnan APC a Arewa Ya Tafka Babban Rashi, Bayanai Sun Fito
- Ana cikin jimami yayin da mahaifin matar gwamnan jihar Neja, Hajiya Fatima Bago ya riga mu gidan gaskiya
- Marigayin Alhaji Muhammad Egba Enagi ya rasu ne a jiya Asabar 9 ga watan Maris a karamar hukumar Edagi
- Rahotanni sun tabbatar da cewa za a yi jana'izar marigayin a yau Lahadi 10 ga watan Maris da misalin karfe 2 na rana
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Neja - Mai sarautar gargajiya a yankin Dikko-Enagi, Alhaji Muhammad Egba Enagi ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 90.
Marigayin da aka fi sani da Sarkin Malami Nupe ya rasu ne a jiya Asabar 9 ga watan Maris.
Wanene marigayin ga matar gwamnan Neja?
Marigayin shi ne mahaifin matar Gwamna Muhammad Umar Bago na jihar Neja, Hajiya Fatima Bago.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, Marigayin shi ne mahaifin matar marigayi tsohon gwamnan jihar, Abdulkadir Kure, cewar Leadership.
Rahotanni sun tabbatar cewa za a gudanar da jana'izarsa a yau Lahadi 10 ga watan Maris da misalin karfe 2 na rana.
Za a gudanar da jana'izar ce a a gidansa da ke Dikko-Enagi da ke karamar hukumar Edati da ke jihar, cewar Housing TV Africa.
Dan bindiga ya mutu yayin daukar kudin fansa
Rundunar ‘yan sanda a jihar Neja ta sanar da kisan wani dan bindiga yayin da yaje daukar kudin fansa a jihar.
Rundunar ta ce ta yi nasarar bindige dan bindigar a karamar hukumar Borgu a jihar yayin da yaje daukar kudin fansa har miliyan uku.
Rahotannin sun tabbatar da cewa dan bindigan ya mutu ne yayin da ya je daukar kudain fansar har miliyan uku a yankin da ke jihar Neja.
Tsohon gwamnan Yobe ya rasu
Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Yobe, Sanata Bukar Abba Ibrahim ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin ya rasu ne a kasar Saudiyya bayan fama da jinya na tsawon lokaci inda aka binne shi a can.
Cikin wadanda suka nuna alhini har da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda ya ce ya rasa babban amini.
Asali: Legit.ng