Kano: Tsohon Kwamandan Hisbah Ya Tona Asirin Wasu ’Yan Siyasa Kan Dambarwar da Ta Faru Kan Hukumar

Kano: Tsohon Kwamandan Hisbah Ya Tona Asirin Wasu ’Yan Siyasa Kan Dambarwar da Ta Faru Kan Hukumar

  • Farfesa Ibrahim Muazzam ya bayyana asalin abin da jawo kace-nace kan matsalar da aka samu tsakanin Hisbah da gwamnati
  • Farfesan ya ce wasu ‘yan siyasa ne marasa kishin jihar ke ruruta lamarin domin kawo rudani a siyasar jihar baki daya
  • Wannan na zuwa ne bayan sulhu da aka yi tsakanin Hisbah da gwamnatin jihar Kano bayan Daurawa ya yi murabus

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Tsohon kwamandan Hukumar Hisbah, Farfesa Ibrahim Muazzam ya soki wasu ‘yan siyasa kan cece-kuce a kamen da hukumar ta yi.

Farfesa Ibrahim ya ce wasu ‘yan siyasa ne suka shirya manakisa wurin ruruta kamen da hukumar ta yi domin batawa mata suna.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya ba hukumar Kwastam sabon umarni kan kayan abincin da ta kwace

Tsohon kwamandan Hisbah ya tona asirin masu neman hada hukumar fada da gwamnati
Farfesa Muazzam ya ce 'yan siyasa ne ke neman kawo rudani a jihar. Hoto: Abba Kabir da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Asali: Facebook

Martanin Farfesan kan hukumar Hisbah

Farfsan ya bayyana haka ne yayin hira da jaridar Daily Trust a jiya Asabar 9 ga watan Maris a birnin Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muazzam ya ce wannan sulhu da aka yi tsakanin Gwamna Abba Kabir da Sheikh Aminu Daurawa ya lalata shirin makiya a jihar.

Ya ce matakin yin sulhu ya lalata duk wani shiri da wasu bata garin ‘yan siyasar ke yi domin hada fada tsakanin hukumar da gwamnatin.

Ya kara da cewa kawai an yi wa matsalar mummunan fahimta ne inda wasu suka yi kokarin yin amfani da damar domin cimma burinsu.

Farfesan ya rike mukamin kwamandan Hisbah ne a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar, Mallam Ibrahim Shekarau.

Ya ce a matsayinsa na wanda ya taba rike Hisbah ya fahimci yadda aka dauki lamarin da girma da yada abun a kafafen sadarwa domin kawo rudanin siyasa a jihar.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Kwastam ta ziyarci Buhari, sun yi magana kan bude iyakoki da Tinubu ke shirin yi

An yi sulhu tsakanin Abba da Daurawa

Har ila yau, Gwamna Abba Kabir da Sheikh Aminu Daurawa sun yi sulhu bayan yin murabus na shugaban hukumar Hisbah.

Sulhun na zuwa ne bayan cece-kuce da aka ta yi bayan Sheikh Daurawa ya ajiye mukamin shugabancin hukumar.

Jama’a da dama sun yi maraba da wannan sulhu inda suke ganin Daurawa zai kara kaimi wurin dakile badala a jihar.

Daurawa ya yi murabus

Kun ji cewa shugaban hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi murabus daga shugabancin hukumar.

Daurawa ya sanar da yin murabus din ne bayan wasu maganganu da Gwamna Abba Kabir ya yi a Kano kan hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.