Shugaba Tinubu Ya Ba Hukumar Kwastam Sabon Umarni Kan Kayan Abincin da Ta Kwace
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumar Kwastam da da dukkan kayan hatsin da ta ƙwace ga masu su
- Babban kwanturolan hukumar, Bashir Adewale Adeniyi, shi ne ya tabbatar da hakan yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki a Katsina
- Adewale ya yi nuni da cewa za a mayar da kayan ne bisa sharaɗin cewa za a sayar da su ne kawai a kasuwannin Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Babban Kwanturolan hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya umurci hukumar da ta mayar da dukkan hatsin da aka kama ga masu su domin ci gaba da sayarwa a kasuwannin Najeriya.
Kwanturolan ya bayyana hakan ne a yayin wani taron masu ruwa da tsaki a garin Kwangwalam da ke kan iyaka da Nijar a ƙaramar hukumar Maiadua ta jihar Katsina ranar Asabar, 9 ga watan Maris 2024, cewar rahoton Daily Trust.
Meyasa Tinubu ya umarci a mayar da kayan?
Ya ce shugaban ya bayar da wannan umarni ne a cikin gagarumin karamcinsa na tabbatar da cewa al’ummar ƙasar nan sun samu isasshen abincin da za su saya a farashi mai rahusa a kasuwanni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce, duk da haka, mayar da kayan abincin da aka ƙwace ga masu su ya dogara ne kawai da sharaɗin cewa za a sayar da su a kasuwannin Najeriya, rahoton Nigerian Tribune ya tabbatar.
"Gaba ɗayan manufar ita ce inganta samar da abinci da kuma tabbatar da cewa ƴan Najeriya ba za su kasance cikin yunwa ba. Shugaban ƙasa na kallon wannan a matsayin ɗaya daga cikin dabarun da za su taimaka wajen magance matsalar ƙarancin abinci.
"Muna da motoci sama da 120 na kayan abincin da za a kai ƙasashen waje da aka kama, wanda hakan ke nufin an fitar da kayan abinci da yawa daga kasuwanninmu, abin da ya kai ƙarancinsu wanda ya haifar ƙaruwar farashin waɗannan kayayyakin.
"Don haka, muna fatan cewa a lokacin da muka dawo da su kasuwanninmu, hakan zai yi tasiri mai kyau a kan farashin."
Kwanturolan ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a mahaifarsa ta Daura da kuma Sarkin Daura, Dr Umar Farouq Umar a fadarsa inda sarkin ya ba shi sarautar gargajiya ta Mabudin Hausa.
Kwastam ta fara sayar da shinkafa
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar kwastam ta fara sayar da shinkafa da sauran kayan abinci a kan farashi mai rahusa a jihar Legas.
Babban kwanturolan hukumar ya bayyana cewa za a sayarwa da talakawa kowane buhun shinkafa mai nauyin 25kg kan kuɗi N10,000.
Asali: Legit.ng