Gwamnan Arewa Ya Tuna da Talakawa, Ya Rage Farashin Kayan Hatsi Saboda Azumi
- Gwamnatin jihar Katsina ta shirya ba talakawan jihar tallafi domin samun sauƙin azumin watan Ramadan
- Gwamnan jihar Malam Dikko Umaru Radda ya ƙaddamar da kwamitin da zai sayar da kayan hatsi kan N20,000 kowane biyu ga mabuƙata
- A ƙarƙashin shirin, gwamnatin za ta kuma raba abinci da kuɗaɗe ga iyalai 33,000 a lokacin watan azumin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - A yayin da ake tsadar kayan abinci a Najeriya, gwamnatin Katsina tare da haɗin gwiwar ƙananan hukumomin jihar 34 sun ware sama da Naira biliyan 10 domin saye da bada tallafin hatsi domin rabawa ga marasa galihu a cikin watan Ramadan.
Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ne ya tabbatar da hakan a yayin ƙaddamar da kwamitocin a matakin jiha da na ƙananan hukumomi da aka ɗorawa alhakin sa ido kan yadda za a raba kayan a ranar Asabar.
A cewar sa, shirin na nufin ciyar da mutane kimanin 72,200 a kullum a cikin watan Ramadan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Talakawa za su samu tallafin abinci a Katsina
Hakan a cewarsa, yana nuna cewa samar da tallafin abinci ga mutane kusan miliyan 2.1 (2,166,000) a tsawon lokacin watan azumin.
Sanarwar da babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar, ta ce shirin ya kuma haɗa da rage farashin masara, gero, da dawa zuwa Naira 20,000 kan kowane buhu.
Domin tabbatar da adalci, gwamnatin ta tsara sayar da kayan hatsin ga mutum biyar duk buhu ɗaya.
Baya ga rage farashin kayan abinci a kan Naira 20,000 kowane buhu, ga kimanin gidaje 400,000, Gwamna Radda ya ce iyalai 33,000 da aka zaɓa daga sassa daban-daban na jihar za su samu kayan abinci kyauta da wasu kuɗaɗe.
Gwamna Radda ya jaddada mahimmancin bin diddigi wajen rabon kayayyakin, inda ya umurci kwamitocin kananan hukumomi da su miƙa kuɗaɗen da aka samu daga sayar da hatsin ga kwamitin jiha domin sakawa a asusun gwamnati.
Legit Hausa ta samu jin ta bakin Yusuf Ahmad wani mazaunin jihar Katsina wanda ya yaba da wannan shirin da Gwamna Radda ya kawo.
Yusuf ya bayyana cewa wannan shirin zai taimaka sosai ga mabuƙata musamman duba da halin ƙuncin da ake ciki yanzu a ƙasar nan.
Ya yi fatan cewa shirin zai kai ga waɗanda aka samar da shi dominsu ba ya maƙale a hannun wasu ƴan tsiraru ba.
Gwamnatin Jigawa za ta ciyar da mutane
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta ciyar da mutane 171,900 a kullum a cikin watan azumin Ramadan na shekarar 1445AH.
Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da rabon kayan tallafin abinci ga mazauna garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa a ranar Juma’a.
Asali: Legit.ng