Gwamnan PDP Ya Dauki Matakin Shari'a Kan Dakataccen Kwamishinan INEC, Bayanai Sun Fito

Gwamnan PDP Ya Dauki Matakin Shari'a Kan Dakataccen Kwamishinan INEC, Bayanai Sun Fito

  • Gwamnatin jihar Adamawa ta ɗauki matakin shari'a kan Yunusa Hudu Ari, dakataccen kwamishinan hukumar zaɓe ta INEC a jihar
  • Gwamnatin jihar tana ƙarar dakataccen kwamishinan zaɓen ne bisa zarginsa da aikata laifukan zaɓe guda uku
  • Hudu Ari dai yana fuskantar tuhume-tuhume kan yadda ya tafiyar da al'amura a lokacin zaɓen gwamnan jihar na shekarar 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Adamawa - Gwamnatin jihar Adamawa ta ɗauki matakin shari'a a kan dakataccen kwamishinan zaɓe na hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) Barr. Hudu Yunusa Ari.

Gwamnatin ta ɗauki matakin ne bisa zarginsa da aikata laifukan zaɓe, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Gwamnatin Adamawa ta shigar da kara kan Hudu Ari
Gwamnatin Adamawa na zargin Hudu Ari da aikata laifukan zabe Hoto: Ahmadu Umaru Fintiri
Asali: Facebook

Gwamnati na neman kotu ta yanke masa hukunci kan wasu sabbin tuhume-tuhume da suka shafi lokacin da yake aiki a hukumar zaɓe a jihar, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya tuna da talakawa, ya rage farashin kayan hatsi saboda azumi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa gwamnatin Adamawa ke ƙarar Hudu Ari?

Gwamnatin jihar ta gurfanar da shi a gaban kotu kan laifuka guda uku da suka haɗa da, dagula zaman lafiyar jama’a, da aikata wasu abubuwa da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya, da kuma yin sojan gonan wani jami’in gwamnati.

Hakazalika, Hudu yana fuskantar tuhume-tuhume shida da gwamnatin tarayya ta shigar, amma an ɗage shari’ar sau da dama saboda rashin gurfanar da shi a gaban kotu.

A yayin zaman kotun, lauyan jihar, Akamode Abayomi, ya shaida wa kotun cewa ba a ba wa wanda ake ƙara takardar kotu ba, duk da ƙoƙarin da suka yi.

Ya bayyana cewa masu gabatar da ƙara na bukatar a sake sanya ranar zaman kotu domin su ƙara azama wajen ba wanda ake ƙara takardun kotu, yana mai tabbatar wa kotun cewa za su yi iya ƙoƙarinsu don gurfanar da shi.

Kara karanta wannan

Malam Radɗa ta bayyana jiha 1 tal da yan bindiga suka fi yawan kai hare-hare a Arewacin Najeriya

Hudu Ari ya shiga hannun ƴan sanda

A baya rahoto ya zo cewa dakataccen kwamishinan zaɓen hukumar INEC na jihar Adamawa, Yunusa Hudu Ari, ya shiga hannun jami'an ƴan sanda.

Ari ya shiga hannu ne bayan jami'an rundunar masu shirye-shirye, sa ido da binciken harkokin da suka shafi zaɓe sun yi caraf da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel