Malamin Musulunci Ya Laftawa Daurawa Laifi a Sabanin Hisbah da Gwamna Abba a Kano

Malamin Musulunci Ya Laftawa Daurawa Laifi a Sabanin Hisbah da Gwamna Abba a Kano

  • Sheikh Sa’id Aliyu Maikwano yana ganin Aminu Ibrahim Daurawa ya yi kuskure da ya samu sabani da gwamnatin Kano
  • A ra’ayin malamin musuluncin da ire-irensa, sam bai dace a bude kofar da za ta jawo a raina gwamna ko wani mai mulki ba
  • Idan kalaman Abba Kabir Yusuf sun fusata Malam Aminu Daurawa, Maikwano ya ce bai dace ya sanar da murabus a fili ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Sheikh Sa’id Aliyu Maikwano ya yi tsokaci a game da sabanin da ya nemi shiga tsakanin Hisbah da gwamnatin jihar Kano.

A wani bidiyo da Sawaba Media ya wallafa a Facebook, an ji shehin ya daura laifi a kan shugaban hukumar Hisbah ta reshen jihar Kano.

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Gwamnan Ribas ya fadi abin da ya yi niyya lokacin shirin tsige shi

Hisbah
Gwamnan Kano da Shugaban Hisbah Hoto: Abba Kabir Yusuf/Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

Sheikh Daurawa ya yi kuskure a Hisbah?

Sheikh Sa’id Aliyu Maikwano yana da ra’ayin cewa bai kamata Aminu Ibrahim Daurawa ya sanar da niyyar murabus gaban duniya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin addinin ya fito a bidiyo a Facebook, ya shaidawa duniya cewa ya ajiye aikin da Mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba shi.

Wannan malami da yake garin Sokoto yana ganin babu ladabi da girmamawa ga gwamnati a yadda Daurawa ya dauki lamarin a fili.

A jawabin da malamin ya yi, ya kara da cewa babu cin mutunci a jawabin gwamnan Kano da ya tunzura shugaban hukumar ta Hisbah.

Hisbah: Maikwano ya ba Abba gaskiya

Sa’id Maikwano yake cewa asali Abba Gida Gida bai ambaci sunan Hisbah ba, illa iyaka ya ce wata hukuma a Kano tana yin ba daidai ba.

Kara karanta wannan

Kano: Jerin albishir 5 da Gwamna Abba ya yi wa Sheikh Daurawa da Hisbah a zaman sulhu

Shehin ya ce abin da ya dace shi ne Malam ya je wajen gwamna, ya nemi ya sauke masa nauyin da ya daura masa, Aminiya ta kawo rahoton.

A cewar malamin, wannan shi ne abin da aka sani a lokacin musulman farko na wannan al’umma, ba a bude kofar cin mutuncin shugaba ba.

Daurawa zai iya jawo a taba gwamna

Maikwano ya yi da’awar cewa matsayar da Daurawa ya dauka a lokacin za su iya jawo a ci mutuncin gwamna, kuma zai samu alhaki.

Kamar yadda aka nada shehin malamin cikin mutunci, Maikwano ya ce kyau ya bar kujerarsa cikin mutunci domin girmama jagora.

Yayin da malamai suka dauki wata matsayar, shehin ya zargi Malam Daurawa da dauko koyawar kungiyar Ikhawan da aka yi a Masar.

Malamai sun sasanta Abba v Hisbah

Sheikh Sani Yahaya Jingir ya fadawa Abba Kabir Yusuf kar a ji kansu da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, a karshe hakan kuwa aka yi.

Malamai da jama’a da yawa sun yi kokari wajen sulhunta Sheikh Aminu Daurawa da gwamna domin ganin an zaunar da tarbiyyah a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng