Sabuwar Matsala Ta Kunno Kai a Gidajen Mai a Birnin Tarayya Abuja, Kamfanin NNPCL Ya Yi Magana

Sabuwar Matsala Ta Kunno Kai a Gidajen Mai a Birnin Tarayya Abuja, Kamfanin NNPCL Ya Yi Magana

  • Ƙarancin man fetur na kara kamari a Abuja yayin da aka fara dogayen layuka ranar Jumu'a, 8 ga watan Maris, 2024
  • Masu ababen hawa da direbobin motocin haya sun haɗa dogon layi a wasu gidajen mai, wasu kuma sun kulle sun daina siyarwa jama'a
  • Kamfanin mai na kasa NNPCL ya bayyana cewa babu wani abun fargaba domin akwai isassen mai a wurinsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ƙarancin man fetur ya ƙara kamari a babban birnun tarayya Abuja yayin da matafiya da direbobin haya suka haɗa dogon layi a gidajen mai ranar Jumu'a.

Yayin da wasu gidajen mai ke fama da dogon layi, wasu gidajen man kuma a kulle suke, an sanya musu kwaɗo an datse.

Kara karanta wannan

"Mijina ya daina kwana da ni a gado" Matar aure ta cire kunya ta fashe da kuka a kotu

An fara dogon layi a gidajen man fetur a Abuja.
Karancin Man Fetur Ya Bayyana a Abuja Yayin da Mutane Suka Yi Layi a Gidajen Mai Hoto: NNPCL
Asali: UGC

Wani direban mota, Chukuemeka Eze, ya shaida wa Premium Times cewa ya shafe sa’o’i hudu a cikin dogon layi a gidan mai a Apo a karkashin rana mai zafi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Eze ya bayyana cewa tun ranar Alhamis ya fahimci akwai layi a gidajen amma duk da haka ya sa a ransa cewa idan ya kama hanyar fitowa Abuja ranar Jumu'a zai tsaya ya siya.

Ya ce:

“Na fito da wuri (8:30 na safe) fiye da yadda na saba da fatan zan samu mai na ci gaba da aikin tsakar rana da karfe 11 na safe, amma ga shi har 1:00 na rana ban siya ba.
"Har yanzun ina fatan samun mai tunda yanzu na samu na shiga gidan man."

Haka nan kuma an kulle ƙofar wani gidan mai Fynefield a yankin Apo, kuma an hana ƙarin motoci su shiga ciki.

Kara karanta wannan

Daliban jami'a 4 sun lakadawa abokin karatunsu duka har ya mutu, ‘yan sanda sun dauki mataki

An haɗa dogon layi a gidan man NNPCL

Dogayen layukan da aka saba yi a ko wanne daga cikin gidajen sayar da man fetur na kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC) Limited na nan yadda aka saba a yau da kullum

Ana haɗa dogon layi a gidajen man NNPCL ne saboda ana sayar da man kan Naira 617 kan kowace lita, kasa da mafi yawan gidajen mai da farashin ke kaiwa N680.

Sauran gidajen man da ke Banex, Apo, Kubwa, da Lugbe a cikin birnin sun sayar da mai akan farashin da ya fara daga N617 zuwa N680.

NNPCL ya yi magana kan ƙarancin mai

Mai magana da yawun kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya shaidawa ƴan jarida cewa babu wani abin fargaba.

"Ba ƙarancin man fetur, muna da tulin mai saboda haka babu wani dalili na fargaba," in ji shi.

Farashin man fetur zai ƙara tashi a Najeriya?

Kara karanta wannan

An kama wasu mata da suka shahara wajen yankan aljihun fasinjoji a Abuja

A wani rahoton kuma kamfanin mai na ƙasa NNPCL ya musanta rahoton da ke yawo cewa farashin man fetur zai ƙara tashi a Najeriya.

Ya kuma shawarci masu ababen hawa da su kaucewa sayen mai da haɗa cunkoso a gidan mai saboda tsoron ƙara farashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262