Farashin gangar mai yayi tashin gwauron zabbi a kasuwannin duniya
- Farashin gangar mai yayi tashin gwauron zabbi a kasuwannin duniya
- Wannan dai ya biyo bayan dambarwar siyasar da yanzu haka take wanzuwa a kasar Iran
- Iran dai na daga cikin manyan kasashen duniya dake hako mai sosai
Rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni ne da cewa farashin gangar danyen mai ta yi tashin gwauron zabo a kasuwannin duniya biyo bayan dambarwar siyasar da yanzu haka take wanzuwa a kasar Iran.
KU KARANTA: Gwamnan Kwara yayi karin haske game da barin APC
Mun samu dai cewa farashin na ganga guda yanzu haka ya kai Dalar Amurka 60.87 wanda ke zaman farashi mafi sama da aka samu cikin shekaru biyu da rabi.
Legit.ng ta samu cewa Iran dai na daga cikin manyan kasashen duniya dake hako mai sosai kuma mamba ce ta kungiyoyin kasashe masu arzikin man fetur.
A wani labarin kuma, Akalla kungiyoyin da ba su gaza dari biyu ba ne wadan da ba na gwamnati ba suka dunkule a karkashin inuwa daya mai suna Non-Governmental Organisations in Nigeria (FONGON) a turance suka kuma tsayar da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari takara a zaben 2019.
Kungiyoyin dai sun bayyana cewa daga sati mai zuwa ne ma za su fara shirya wani babban gangami da zai samu halartar manya daga cikin shugabanni da kuma mambobin su domin ganin shugaban ya tsaya takara.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng