Malam Radɗa Ya Bayyana Jiha 1 Tal da Ƴan Bindiga Suka Fi Yawan Kai Hare-Hare a Arewacin Najeriya
- Gwamna Dikko Umaru Radɗa ya ce jihar Katsina ta fi ko ina fama da hare-haren ƴan bindiga a shiyyar Arewa maso Yamma
- Malam Raɗɗa ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da ɗaukar matakai domin kawar da ƴan bindiga a jihar Katsina
- Ya yi wannan jawabin ne yayin da ya karɓi bakuncin shugaban hukumar NCFRMI a ofishinsa ranar Jumu'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya bayyana cewa jihar Katsina ce a sahun gaba wajen fama da hare-haren ƴan bindiga da garkuwa domin neman kuɗin fansa.
Gwamnan na jihar Katsina ya ce jiharsa ta fi dukkan jihohin Arewa maso Yamma fuskantar hare-haren ta'addancin ƴan bindiga, kamar yadda Leadership ta tattaro.
Daga nan Gwamna Raɗɗa ya roki gwamnatin tarayya ta duba yuwuwar kafa cibiyar sana'o'i da ta fara tunanin kafawa a baya domin tallafawa waɗanda ƴan bindiga suka taɓa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dikko Raɗda ya yi wannan furucin ne yayin da ya karbi bakuncin kwamishinan hukumar kula da ‘yan gudun hijira da baƙin haure (NCFRMI), Tijjani Aliyu a ofishinsa ranar Juma’a.
Mai girma gwamnan ya roƙi karin haɗin kai da goyon baya domin tallafawa ƴan gudun hijira a jihar Katsina.
Wane hali ake ciki kan matsalar ƴan bindiga a Katsina?
Gwamna Radda ya kuma yi Allah wadai da sababbin hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a yankunan da ke kusa da babban birnin jihar, inda ya bayyana su da abin takaici.
Amma duk da haka ya jaddada kudirin gwamnatinsa da ɗaukar matakan kakkaɓe ‘yan bindiga a jihar, Premium Times ta rahoto.
Da yake mika godiya ga kwamishinan NCFRMI bisa ziyarar da ya kai masa, gwamnan ya ce gwamnatinsa zata ci gaba da kokarin tallafawa mutanen da hare-haren ‘yan bindiga ya shafa a jihar.
Dalilin da ya sa kwamishinan NCFRMI ya je Katsina
A nasa jawabin, kwamishinan NCFRMI, Tijjani Aliyu, ya ce sun kawo ziyara ne domin kaddamar da rabon kayan abinci ga mata 700 da ke gudun hijira a jihar.
Ya ce gwamnati ba za ta ci gaba da samar da kayan tallafi ga ‘yan gudun hijira ba, shiyasa take kokarin kafa cibiyoyin koyar da sana'a domin ƴan gudun hijira su dogara da kansu.
Sojoji sun halaka ƴan ta'adda 210 a mako guda
A wani rahoton kuma Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi nasarar halaka ƴan ta'adda 210 tare da kamo wasu 142 da ceto mutum 46 da aka yi garkuwa da su.
Hedkwatar tsaro ta ƙasa DHQ ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar kan nasarorin da sojoji suka samu a mako ɗaya da ya gabata.
Asali: Legit.ng