Yan Sanda 4 Sun Mutu Yayin da Mahara Suka Yi Ajalinsu, Harin Ya Rusa da 'Yan Matansu 2
- Jama'a sun shiga rudani yayin da wasu 'yan bindiga suka yi ajalin wasu jami'an 'yan sanda guda hudu a jihar Ebonyi
- Maharan sun kuma hallaka wasu mata guda biyu da ake zargin 'yan matan jami'an tsaron ne da suka mutu
- Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da safiyar yau Juma'a 8 ga watan Maris a birnin Abakaliki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ebonyi - 'Yan bindiga sun yi ajalin wasu jami'an 'yan sanda guda hudu a jihar Ebonyi da ke Kudancin Najeriya.
Lamarin ya faru ne a yau Juma'a 8 ga watan Maris da misalin karfe 5:00 na safe a birnin Abakaliki da ke jihar, cewar Leadership.
Harin ya kuma rutsa da mata biyu
Har ila yau, wasu mata guda biyu sun rasa rayukansu yayin harbe-harben 'yan bindigan wanda ya rutsa da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani shaidan gani da ido ya shaidawa Punch cewa maharan sun dawo ne daga wani aiki inda suka bude wuta.
Majiyar ta ce harin 'yan bindiga ya yi sanadiyar mutuwar jami'an 'yan sanda guda hudu da kuma mata guda biyu.
"Yankinmu ya zama abin tsoro, da safen nan wani lamari ya faru inda 'yan sanda suka hallaka jami'an 'yan sanda.
"Kuma kun sani irin wannan lamari ya faru a daidai wurin a shekarar da ta gabata inda harin ya yi ajalin 'yan sandan.
"Wandanda suka mutu bara har yanzu ba a binne su ba sai gashi wasu shida sun sake mutuwa da mata guda biyu."
- Cewar majiyar
Martanin rundunar 'yan sanda kan harin
Majiyar ta ce ana zargin 'yan matan jami'an 'yan sandan ne da suka mutu harin suma ya rutsa da su, cewar Ripples.
Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, DSP Ukandu Joshua ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Juma'a 8 ga watan Maris.
Kasurgumin dan bindiga ga shiga hannu
Kun ji cewa rundunar 'yan sanda a birnin tarayya ta yi nasarar cafke kasurgumin dan bindiga da ya addabi birnin.
Rundunar ta ce ta yi nasarar cafke dan bindigan ne bayan samun bayanai sirri inda suka tabbatar ya kware wurin garkuwa da mutane.
Asali: Legit.ng