Gwamnati Ta Kaddamar da Gina Titi Mai Nisan 700km a Kudu, Zai Lashe Maƙudan Kuɗaɗe

Gwamnati Ta Kaddamar da Gina Titi Mai Nisan 700km a Kudu, Zai Lashe Maƙudan Kuɗaɗe

  • Gwamnatin tarayya ta fara aikin gina babban titin bakin teku daga Legas zuwa Kalaba mai tsawon kilomita 700
  • Kamfanin gine-gine na Hitech ne aka ba aikin gina titin wanda zai ratsa ta jihohi tara, tare da kai wa ga wasu jihohin Arewa
  • Gwamnatin ta kuma fara gyaran manyan gadoji a Legas da suka hada da gadar Queen's Drive Ikoyi da gadar Third Mainland

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Gwamnatin tarayya ta fara aikin gina babban titin bakin teku daga Legas zuwa Kalaba mai tsawon kilomita 700 tare da gyaran manyan gadoji a Legas.

Ministan ayyuka, Nweze David Umahi, a lokacin kaddamar da aikin kashi na farko ya ce gwamnati ba za ta amince da jinkiri ko tafiyar hawainiya ba da zarar an fara aikin.

Kara karanta wannan

Buga kudi: Yadda Buhari ya jawo hauhawar farashin kaya, Ministan Tinubu ya magantu

Ministan ayyuka, Nweze David Umahi
Gwamnati za ta gina titi daga Legas zuwa Kalaba mai tsawon kilomita 700. Hoto: @FMWNIG
Asali: Twitter

Babban titin bakin teku tsakanin Legas da Kalaba zai ratsa ta jihohi tara, kuma wani bangare na titin zai kai ga wasu jihohin Arewa, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ba kamfanin Hitech kwangilar aikin

Wata sanarwa da mai bai wa ministan shawara kan harkokin yada labarai, Orji Uchenna, ya fitar, ta ce za a shimfide titin ne da zallar kankaren siminti.

Leadership ta bayyana cewa kashi na farko na aikin wanda aka ba kamfanin gine-gine na Hitech aikinsa zai lashe tsawon kilomita 47.47, kuma za a yi shi a tsarin hannu biyu.

Ministan ya jaddada bukatar daukacin ‘yan kwangilar da ke kula da ayyukan titunan gwamnatin tarayya da su rinka kammala ayyukansu akan lokaci.

Gwamnati ta fara gyaran gadojin Legas

Sai dai Vanguard ta ruwaito ministan na yabawa kamfanin 'Hitech Construction Nigeria Ltd' saboda inganci da kuma kammala ayyuka a kan lokaci.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya amince a gaggauta raba wa mazauna Abuja kayan abinci

Ministan ya kuma ziyarci gadar Queen's Drive Ikoyi, gadar Third Mainland, gadar karkashin ruwa, gadar Eddo, gadar Eko da gadar Carter da ake gudanar da gyare-gyare a kansu.

Ya bayyana aniyar gwamnatin tarayya na gudanar da aikin gyaran gadojin kasancewar suna da matukar muhimmanci a tsakanin yankin Mainland da tsibirin Legas.

Minista ya yi kokarin aikin titin Imo

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa ministan ayyuka, David Umahi ya yi wa kamfanin Fig Fyne Construction Company tatas kan gina titi maras kyau.

Rahotanni sun bayyana cewa ran ministan ya baci kuma ya yi Allah-wadai da kamfanin ka yadda ya yi ha'inci a gina titin na Amanwozuzu-Uzoagba-Eziama-Orie-Amakohia.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.