Gwamnatin Tarayya zata gyara babbar gadar Third Mainland Bridge ta Legas - Fashola
Kwamitin zababbu na Gwamnatin tarayya sunyi taron awa takwas a ranar laraba don amincewa da fitar da Naira biliyan 18.874 don gyaran babbar gida ta uku a jihar Legas, Gadar ta Legas, tafi kowacce gada tsawo a kan ruwa a fadin kasar nan
Ministan aiyuka, wuta da kuma gidaje, Babatunde Fashola, ya bayyana hakan a tsokacin da yayi ma manema labarai bayan kammala taron FEC wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya shugabanta.
Ministan yace an ba ma wani kamfanin kwangila ne na kasar Italia mai suna, Borini Prono, wanda su sukayi gadar.
Yace kashi 33 na gadar za a maye gurbin su da wasu a farkon aikin, karafuna 177 kuma za a mikar dasu.
Fashola ya roki zuba hannun jari ta bangaren wutar lantarki. Ya kara da cewa kwangilar zata hada da fadada hadin gadar tare da canje canje a inda yakamata.
DUBA WANNAN: Sojin Amurka a Najeriya?
Yace kwangilar da zata dau tsawon watanni 27 an kalle ta a matsayin "kwangilar gyara gada" a cikin tsarin shekara 2018 wanda ba a zartar ba.
Ministan yace koda dai Gwamnatin da ta gabata ta karbi jinjinar kwangilar a 2011, amma bata saka hakan a tsarin ta ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng