Mun kawar da ta'addanci a Najeriya, Hedkwatar tsaro DHQ

Mun kawar da ta'addanci a Najeriya, Hedkwatar tsaro DHQ

- Tun da an daina kai hare-haren kunar bakin wake, mun samu nasara, kakakin hedkwatar tsaro ya bayyana

- Hukumar Soji ta yi ikirarin kawo karshen ta'addanci a Najeriya

Hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta ce jaruman Sojojin Najeruya sun dakile yan ta'addan Boko Haram da abubuwan da suke yi a Arewa maso gabashin Najeriya.

Amma fa duk da wannan ikirari da hukumar ke yi, har yanzu yan ta'adda na kai hare-hare yankin Arewa maso gabas.

Ba da dadewa ba yan ta'addan Boko Haram suka kai hari kan manoma a Zabarmari, a jihar Borno inda suka kashe akalla manoma 40.

Amma yayin hira a kamfanin dillancin labarai NAN ranar Litinin, jagoran yada labarai na hedkwatar tsaro, ya ce gwamnatin tarayya da Sojoji sun kawar da hare-haren yan ta'addan tun shekarar 2015 a fadin tarayya - musamman arewa maso gabas.

Ya ce yanzu yan Boko Haram sun daina bayyana makamai da iko fili kamar yadda suke yi a bayan, kuma babu wani yanki na Arewa dake karkashin yan ta'addan.

"Kai harin bama-bamai wurare irin Abuja, Kano, Niger da Kogi da kafa sansani duk duk babu yanzu," yace.

"Hakazalika kunar bakin wake, wanda yana daya daga cikin alamomin ta'addanci. A baya har wuraren da muke zaune suke zuwa tayar da Bam, har da wuraren taro, duk mun kawar da wannan yanzu."

"Idan ka hada wadannan abubuwa, ina tabbatar maka an kawar da ta'addanci.

"Amma duk da haka, akwai barbashin hare-hare nan da can; mai kama da ta'addanci."

KU KARANTA: Yayinda aka gano wasu a Anambra da Enugu, an sake sace wani yaro a Kano

Mun kawar da ta'addanci a Najeriya, Hedkwatar tsaro DHQ
Mun kawar da ta'addanci a Najeriya, Hedkwatar tsaro DHQ Hoto: Channels TV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dokta Bashir: Idan mutum ya saki matarsa a shirin fim to ya saki matarsa ta gida ne

A bangare guda, 'yan bindiga sun kashe dan takarar kansila na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben da za a gudanar a ranar 6 ga watan Maris a Delta, Mista Elliot Ofa.

The Nation ta ruwaito cewa yan bindigan sun sace wasu mutane biyu tare da shi.

Sai dai a tabbatar ko kashe shi na da alaka da siyasa ba sakamakon wasu na zargin cewa tun farko wasu basu so aka nada shi a jam'iyyar ta PDP.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel