Sojojin Najeriya Sun Aike da Muhimmin Saƙo Ga Musulmai Yayin da Ake Shirin Fara Azumin Ramadan
- Hedikwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta bayyana cewa sojoji sun shirya tunkarar kowace irin barazana musamman a watan Ramadan
- A wata sanawar da DHQ ta fitar ranar Jumu'a, ta ce sojoji ba zasu yi kasa a guiwa ba sai sun ga bayan ƴan ta'adda baki ɗaya a kasar nan
- Hediwata ta ce sojoji mutane ne masu son zaman lafiya, za su yi duk mai yiwuwa wajen samar da kwanciyar hankali a ko ina ake buƙata
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Hedikwatar tsaro (DHQ) ta ce dakarun sojojin da aka tura a fadin Najeriya sun shirya tsaf domin tunkarar duk wata barazanan tsaro a kasar nan.
DHQ ta kuma tabbatar da cewa sojojin a shirye suke su tunkari duk wata barazana musamman a lokacin da al'ummar musulmi ke shirin fara azumin watan Ramadan.
Jaridar Punch ta tattaro cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun DHQ na ƙasa, Manjo Janar Buba Edward, ya fitar ranar Jumu'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce dakarun sojoji sun shirya kuma za su iya magance duk wata barazanar tsaro a tsawon lokacin da za a shafe ana azumtar watan Ramadan.
"Yayin da ake shirye-shiryen fara azumin watan Ramadan, dakarun sojoji sun shirya tunkarar kowace irin barazana kuma sun san yadda za su kawar da ita.
Mun shirya kawo karshen ta'addanci - DHQ
Buba ya kuma sha alwashin cewa sojojin ba za su yi kasa a gwiwa ba ko su huta har sai sun kakkaɓe ‘yan ta’adda gaba ɗaya a fagen daga.
A rahoton Leadership, ya ce:
“Sojoji za su ci gaba da kakkaɓe ‘yan ta’adda da masu taimaka masu da ke fagen daga tare da korarsu daga wuraren da suka ɓuya a fadin kasar nan.
"Rundunar sojoji tana kaunar zaman lafiya kuma tana kokarin tabbatar da kwanciyar hankali a duk inda buƙatar hakan ta taso a faɗin kasar nan.
"Saboda mun shirya tsaf kuma muna nan kan bakarmu na kare kasar nan da mutanen cikinta."
Uba Sani ya yi magana kan manyan matsaloli 2
A wani rahoton kuma Malam Uba Sani ya bayyana cewa hanyoyin da ake bi da nufin magance talauci da matsalar tsaro a Najeriya kuskure ne.
Gwamnan ya ce waɗannan kalubalen biyu sun zama alaƙaƙai da ke damun shugabannin siyasa a halin yanzu.
Asali: Legit.ng