Daliban Jami'a Sun Lakadawa Abokin Karatu Duka Har Ya Mutu, ’Yan Sanda Sun Dauki Mataki

Daliban Jami'a Sun Lakadawa Abokin Karatu Duka Har Ya Mutu, ’Yan Sanda Sun Dauki Mataki

  • Wasu dalibai hudu da ba a bayyana sunayensu ga manema labarai ba sun kashe abokin karatunsu ta hanyar lakada masa duka
  • Rahotanni sun ce dalibin ya gamu da ajalinsa ne bayan da abokan hudu suka kama shi yana nadar bidiyon su, lamarin da ya ja suka duke shi
  • Jami’in hulda da jama’a na 'yan sanda, Toun Ejire-Adeyemi (DSP), ya tabbatar da afkuwar lamarin tare da fadin matakin da aka dauka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ilorin, jihar Kwara – Wasu daliban jami’ar jihar Kwara (KWASU), Malete, da ke karamar hukumar Moro a jihar sun yi wa wani dalibi dukan tsiya har ya mutu.

Jami'an rundunar 'yan sanda
Yan sanda sun kama daliban da suka kashe abokin karatunsu a KWASU. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Vanguard ta ruwaito cewa an kama daliban ne a ranar Laraba, 6 ga watan Maris, amma lamarin ya faru ne a makon da ya gabata a daya daga cikin gidajen kwanan daliban.

Kara karanta wannan

Sace ƴan firamare: An gano yawan daliban da aka yi garkuwa da su a Kaduna

Yadda aka yi wa dalibin KWASU duka har lahira

Daily Trust ta ruwaito daliban sun dura kan marigayin, wanda har yanzu ba a san sunansa ba, bisa zargin yana yi masu bidiyo a sirrance.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce sun tambaye shi dalilin da ya sa yake yi masu bidiyo ba tare da izininsu ba, wanda ya gaza ba da wata 'kwakkwarar hujjar yin hakan'.

Wani dalibi da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa“daga baya dalibin ya mutu sakamakon tsananin duka da daliban suka yi masa.”

‘Yan sanda sun yi karin haske kan lamarin

NAN ta ruwaito jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi (DSP), ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, 7 ga Maris, 2024.

A cewarta:

“Wadanda ake zargin su hudu ne, amma ba zan iya ba da sunayensu ba a yanzu. An kama su ne yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.”

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Gwamnan Ribas ya fadi abin da ya yi niyya lokacin shirin tsige shi

EFCC ta kama daliban KWASU guda 48

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa, hukumar EFCC ta kama dalibai 48 na jami'ar jihar Kwara (KWASU), akan laifin zamba ta 'intanet'.

Dele Oyewale, kakakin hukumar, wanda ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya ce an kama daliban ne bayan tattara bayanai kan laifukan da suke aikatawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.