Kotu Ta Sake Dakatar da Abba da Majalisar Kano da Aiwatar da Wani Muhimmin Ƙudiri

Kotu Ta Sake Dakatar da Abba da Majalisar Kano da Aiwatar da Wani Muhimmin Ƙudiri

  • Yayin da majalisar jihar Kano ke kokarin gyaran fuska a dokokin wasu hukumomi, kotu ta taka mata birki
  • Majalisar ta na yunkurin sauya fasalin dokokin hukumomin ne don inganta yadda za a gudanar da su
  • Hukumomin sun hada da na asusun kula da shari'a da na fansho da hukumar majalisar dokokin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Babbar kotu da ke jihar Kano ta dakatar da majalisar jihar kan gyaran fuska a dokokin wasu hukumomi guda uku, cewar Daily Trust.

Hukumomin uku da ake tabata a kai sun hada da na asusun kula da bangaren shari'a da hukumar fansho da giratuti da kuma hukumar majalisar dokokin jihar.

Kara karanta wannan

An garkame fursunoni 300 a gidan yarin Kano ba tare da aikata laifin komai ba, in ji ‘yan sanda

Kotu ta yi hukunci kan gwamnatin Abba Kabir da majalisa kan gyaran fuska a wasu dokoki
Kotun ta ba da umarnin dakatar da kudirin zuwa bayan sauraran karar. Hoto: Kano State House of Assembly, Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Wane mataki kotun da dauka kan majalisar da Abba?

Alkalin kotu, Mai Shari'a, Usman Mallam Na'Abba shi ya yanke wannan hukunci bayan lauyan masu shigar da kara, M. I Umar ya gabatar da korafi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin ya yi hukuncin ne bayan karbar takardar da shugaba kungiyar ma'aikatan shari'a da sakatarenta sun yi rantsuwa kan takardar da ke dauke da shafuka 19.

"Wannan umarni ya na nufin dakatar da ci gaba da kokarin gyaran fuska kan dokokin da ake magana a kansu.
"Saboda haka an dakatar da majalisar da sauran wadanda ake kara kan wannan kudirin har sai bayan sauraran korafin da ke gaban kotun."

- Usman Na'Abba

Jerin wandanda ake kara kan dokar

Daga cikin wadanda ake karar akwai Gwamna Abba Kabir Yusuf da kwamishinan shari'a a jihar da kuma majalisar jihar, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Duk da halin kunci da ake ciki, Kwastam ta sake cafke tirela makare da kayan abinci zuwa ketare

Sauran sun hada da kakakin majalisar da mataimakinsa da shugaban masu rinjaye da kuma shugaban marasa rinjaye a majalisar.

Har ila yau, wata kotu a jihar Kano ta yi hukunci kan badakalar dala da ake zargin tsohon gwamna Abdullahi Ganduje da aikatawa.

Kotun ta yi hukunci inda ta ce hukumar yaki da cin hanci a jihar ba ta da hurumin ci gaba da bincike ko hukunta Ganduje kan badakalar.

Tinubu ya ba Abba Ganduje mukami

Kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya ba Abba Ganduje mukamin darekta a hukumar REA.

Abba ɗa ne ga shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje wanda ya yi gwagwarmaya a kafa gwamnatin Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.