Sace Ƴan Firamare: An Gano Yawan Daliban da Aka Yi Garkuwa da Su a Kaduna
- Akalla dalibai 287 ne 'yan bindiga suka yi awon gaba da su yayin da suka kai farmaki a wata makarantar firamare da ke Kuriga, jihar Kaduna
- Shugaban makarantar, Sani Abdullahi, wanda ya sha da kyar a hannun 'yan bindigar, ya tabbatar da adadin ga Gwamna Uba Sani
- Idan ba a manta ba, a jiya Alhamis, Legit Hausa ta ruwaito maku yadda 'yan bindigar suka bude wuta a makarantar tare da sace daliban
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kaduna - Shugaban makarantar firamare ta LEA da ke Kuriga a karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna, Sani Abdullahi ya tabbatar da cewa dalibai 287 na makarantar ne wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da su.
TVC News ta ruwaito cewa Mallam Abdullahi na daga cikin wadanda 'yan bindigar suka yi awon gaba da shi amma daga baya ya tsere tare da wasu dalibai.
Yadda aka sace dalibai da kashe dan banga - Abdullahi
Shugaban makaranta ya ba da labarin yadda 'yan bindiga suka sace dalibai 287 a Kaduna
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ziyarar Gwamna Uba Sani, Abdullahi ya bayar da bayanai, inda ya shaida cewa an sace dalibai 187 na sashen sakandare da 125 daga bangaren firamare, inda 25 suka kubuto.
Ya kuma bayyana cewa an kashe wani dan banga da ya yi yunkurin ceto wadanda abin ya shafa wanda tuni aka yi jana'izar shi.
Gwamna Uba ya daukar wa iyayen daliban alkawari
A ziyarar tasa, Gwamna Uba Sani ya tabbatar wa al’umma cewa gwamnati ta dukufa wajen ganin an dawo da daliban da aka yi garkuwa da su ba tare da an samu matsala ba.
Arise TV ta wallafa bidiyon ziyarar gwamnan zuwa garin na Kuriga, tare da duba makarantar da aka yi garkuwa da dalibanta.
Kalli bidiyon a kasa:
Yan bindiga sace dalibai a makarantar Kuriga
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa ‘yan bindiga suka kai hari a makarantar firamare ta LEA, da ke garin Kuriga, a karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna.
Wani mazaunin Kuriga, Shitu wanda ya tabbatar da kai farmakin, ya ce daliban sun yi yunkurin guduwa a lokacin da suka hango ‘yan bindigar a harabar makarantar.
Shi ma wani mazaunin garin Lawal Kuriga, ya shaida wa manema labarai cewa 'yan bindigar sun tafi da daliban da suka sace zuwa cikin daji.
Asali: Legit.ng