Ma’aikatan Akwai Ibom Sun Ce Lallai N800, 000 Za Su Karba a Mafi Karancin Albashi
- Kungiyar kwadago a jihar Akwa Ibom ta bukaci N850,000 a matsayin karancin albashin ma’aikata a jihar
- Shugaban NLC a jihar, Kwamrad Sunny James, ya ce ya kamata a aika duk gwamnan da ya ki biyan N850,000 magarkama
- Sakataren kungiyara jihar, Kwanrad Kinsley Bassey, ya ce ana biyan ma’aikatan Najeriya albashin bauta ne duba ga tsadar rayuwa da ake ciki
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Uyo, jihar Akwa Ibom – Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun bukaci a biya ma’aikatan jihar Akwa Ibom N850,000 a matsayin mafi karancin albashi.
Shugaban kungiyar NLC na jihar, Kwamared Sunny James ne ya bayyana haka yayin taron jin ra’ayin jama’a da gwamnatin tarayya ta shirya kan mafi karancin albashi a garin Uyo, a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris.
Mista James ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda har yanzu wasu jihohin yankin ba su fara aiwatar da mafi karancin albashi na N30,000 wanda aka sake nazari a shekarar 2019, rahoton Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A garmake duk gwamnan da ya ki biya, James
Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, James ya ce ya kamata a jefa duk gwamnan da ya ki biyan N850,000 a gidan yari.
“Duk gwamnan jihar da ya ki biyan sabon mafi karancin albashi toh a daure shi.”
Sakataren kungiyar na jihar, Kwamrad Kinsley Bassey ya ce gwamnatin Najeriya na biyan ma’aikata albashin bauta.
"A matsayinmu na ma'aikatan Najeriya, muna samun albashin bauta ne idan aka yi la'akari da tsadar rayuwa."
TUC da NLC sun sha bamban a Abuja
A gefe guda, mun ji cewa kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta gabatar da N709,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikata a ƙasar nan.
Ƙungiyar ta gabatar da wannan adadin kudi ne a wurin taron jin ra'ayoyin jama'a kan mafi ƙarancin albashin ma'aikata a birnin tarayya Abuja ranar Alhamis.
A daya bangaren kuma kungiyar ‘yan ƙwadago (TUC) ta bada shawarar N447,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi.
Asali: Legit.ng