'Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴan Sanda da Bankuna 2, Sun Tafka Mummunar Ɓarna
- Ƴan bindiga sun farmaki ofishin ƴan sanda da bankuna biyu a jihar Kogi, sun kashe ɗan sanda ɗaya da wani bawan Allah mai talla a bakin titi
- Ganau sun bayyana cewa maharan sun biyo wata motar ɗauko kudi daga wani banki, kuma sun kwashe adadi mai yawa da ba a tantance ba
- Bayan nan kuma ƴan fashin sun fasa wani bankin dabam, sun sace kuɗi masu yawa da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin Alhamis
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Wasu ‘yan bindiga sun kai hari bankuna biyu a garin Anyigba da ke karamar hukumar Dekina a jihar Kogi, inda suka kashe ɗan sanda daya da wani bawan Allah.
Wani faifan bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya ya nuna cewa ‘yan bindigar sun kai mummunan hari kan bankunan da misalin karfe 5 na yammacin Alhamis.
Ganau sun ce maharan sun buɗe wuta a bankunan wadanda sun shahara da kuma caji ofis din garin, kana suka yi awon gaba da makudan kuɗin da ba a tantance adadinsu ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda mahara suka farmaki caji ofis
‘Yan fashin da suka shiga garin sun fara kai farmaki ofishin ‘yan sanda da ke kan titin Anyigba-Idah, inda suka kashe dan sandan da aka bayyana sunansa da Idoko.
Majiyar ta ce ɗan sandan da aka kashe bai jima da komawa aiki a ofishin ba kuma ya fito ne daga Iyale, wani gari da ke makwabtaka da karamar hukumar, Channels tv ta tattaro.
Bayan haka kuma ƴan fashi da makamin sun kashe wani mutumi mai suna, Alagama, wanda yana talla a bakin titi, ba zato harsashin maharan ya yi ajalinsa.
Ɓarnar da maharan suka yi a bankuna
Ganau ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun biyo motar ɗauko kuɗin bankin zuwa ofishinsu da ke Anyigba, inda suka ci ƙarfin jami’an tsaro kafin su kwashe duka kudaden.
Bugu da ƙari, wata tawaga da ake zaton tana cikin ƙungiyar ƴan fashin ta kutsa kai cikin wani fitaccen banki da ke garin, nan ma suka yi awon gaba da kuɗi masu yawa.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar Kogi (PPRO) SP William Aya, bai amsa kira ko sakon da aka aika masa kan lamarin ba, Daily Trust ta rahoto.
Jirgin NAF ya gamu da haɗari a Kaduna
A wani rahoton kuma jirgin atisaye 'Super Mushshak' na rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) ya gamu da hatsari a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, 2024.
Mai magana da yawun NAF, AVM Edward Gabkwet, ya ce matukan da ke cikin jirgin, waɗanda ke dawowa daga ɗaukar horo, sun tsira daga hatsarin.
Asali: Legit.ng