Sabon bidiyo ya billo inda yan ta’addan Boko Haram suka kai hari ga sojojin Najeriya

Sabon bidiyo ya billo inda yan ta’addan Boko Haram suka kai hari ga sojojin Najeriya

- Wani sabon bidiyo dake nuna yan ta’addan Boko Haram suna kashe sojoji a jihar Adamawa ya billo

- An ce bidiyon ya kuma nuna inda kananan mayakan Boko Haram suka yi tuki zuwa sabon Gari kafin harin

- Sai dai duk kokarin Legit.ng na samun martani daga kakakin rundunar sojin Kanal SK Usman bai samu ba

Wani sabon bidiyo da ake zargin bangaren Abubakar Shekau na Boko Haram sun samar da wani bidiyo dake nuna yan ta’addan Boko Haram suna kashe wasu sojoji a Sabon Gari, wani kauye a karamar hukumar Madagali na jihar Adamawa ya billo a cewar Sahara Reporters.

Sahara Reporters sun ruwaito cewa mummunan harin, ya afku ne a makon da ya gabata, an gano mayakan na amfani da wasu makaman soji da kungiyar Boko Haram suka kwato a lokacin wani hari mara nasara da yan ta’addan suka gwabza da sojoji a dajin Sambisa a ranar 10 ga watan Nuwamba.

Legit.ng ta tattaro cewa sabon bidiyon, wanda ya kai tsawon mintina takwas da sakon 56, ya nuna inda kananan mayakan Boko Haram suka yi tuki vikin Sabon Gari kafin harin. Zuwansu kauyen ya biyo bayan wani musayar wuta da sojojin Najeriya.

Sabon bidiyo ya billo inda yan ta’addan Boko Haram suka kai hari ga sojojin Najeriya
Sabon bidiyo ya billo inda yan ta’addan Boko Haram suka kai hari ga sojojin Najeriya

Bidiyon ya kuma nuna gawawwakin sojoji da aka kashe a harin.

KU KARANTA KUMA: Atiku ya bayyana hanyoyin da za a iya kawo karshen hare-haren kunar bakin wake a Najeriya

Harin na Sabon Gari, yace Ahmad Salkida, wani dan jarida kuma gwanin Boko Haram, ya kuma bayyana cewa har yanzu kungiyar na da ikon kai munanan hare-hare duk da cewan sojoji na toshe hanyoyinsu, wanda ya hana yan Boko Haram samun damar sun makamai daga kasashen Afrika ta kudu da tsakiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng