Shugaban Kungiyar Fulani, Miyetti Allah Ya Kai Karar Gwamnatin Tarayya, an Samu Karin Bayani
- Shugaban kungiyar Miyetti Allah, Bello Bodejo, ya roki wata babbar kotun tarayya da ke Abuja da ba gwamnati umarnin a sake shi
- Lauyan Bodejo, Mohammed Sheriff, ya shaida wa kotun cewa, hukumar tsaro ta NIA ta kulle Bodejo na tsawon kwanaki 43 ba tare da tuhuma ba
- Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta ruwaito cewa an kama Bodejo ne a ranar 23 ga watan Janairu bayan kaddamar da 'yan bangar Fulani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah da ake tsare da shi, Bello Bodejo, ya shigar da gwamnati kara a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Daily Trust ta ruwaito Bello Bodejo na neman kotun ta ba da umarnin a sake shi ba tare da wani sharadi ba daga hannun hukumar leken asiri ta kasa.
Bodejo ya shafe kwanaki 43 a tsare
Lauyan Bodejo, Mohammed Sheriff, ya shaida wa kotun cewa, sun gabatar da bukatar ne bisa dogaro tauye 'yancinsa da hukumar ta yi na kin sakinsa gabanin zuwa kotu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya shaida wa kotun cewa duk da umarnin kotu, wanda yake karewa (Bodejo) ya shafe kwanaki 43 a tsare ba tare da an gurfanar da shi a gaban wata kotun da ke da hurumi ba.
Y. A. Imana, kamar yadda The Punch ta ruwaito, ita ce ke kare Antoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a a gaban kotun, kuma ta yi martani kan bukatar Sheriff.
Martanin da gwamnati ta yi kan bukatar
Imana, ta shaida wa kotun cewa wasu matsaloli ne suka sa har yanzu hukumar NIA ba ta aika takardar Bodejo zuwa ga ma’aikatar ba.
Ta ce bayan wasiku uku zuwa ga NIA, sarkakiyar da ke a cikin binciken da suke yi ya sa sun gaza ba da takardun da za su iya gurfanar da Bodeji a gaban kotu.
Channels TV ta ruwaito Mai shari’a Inyang Ekwo, ya dage zaman shari'ar zuwa ranar 13 ga Maris don sauraron karar da Badejo ya shigar.
Dalilin da ya sa aka kama Bodejo
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa an kama Bodejo ne a ranar 23 ga watan Janairu a ofishin Miyetti Allah da ke karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa.
A kama shugaban Fulanin ne sakamakon kaddamar da kungiyar ‘yan bangar Fulani da ta yi ba tare da ya samu izini daga hukumar gwamnati ba.
Asali: Legit.ng