“Kudin Siminti Ya Ragu Zuwa N7,800”: ‘Dan Kasuwa Ya Kira Kwastama Ya Maida Masa Ragin N400

“Kudin Siminti Ya Ragu Zuwa N7,800”: ‘Dan Kasuwa Ya Kira Kwastama Ya Maida Masa Ragin N400

  • Wani 'dan Najeriya ya siya kowani buhun siminti kan N8,200 a jihar Kaduna, inda yake da zama
  • Sai dai kuma, lokacin da ya isa gida, ya samu kira daga wajen mai siyar da simintin yana sanar da shi cewa an rage farashin zuwa N7,800 kowani buhu
  • Abdulaziz Rogo ya ce ya yi mamaki lokacin da mai sayar da simintin ya mayar masa da cikon kudinsa N400 harma da kiransa bayan ya bar shagon

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wani mutumi ya siya siminti kan N8,200 kowani buhu a Kano sannan ya bayyana yadda lamarin ya kaya a dandalin Facebook.

Wannan Bawan Allah, Abdulaziz Rogo ya ce ya tafi da simintin gida, kwatsam sai ya samu kiran waya daga mai siyar da kayan.

Kara karanta wannan

Buga kudi: Yadda Buhari ya jawo hauhawar farashin kaya, Ministan Tinubu ya magantu

Matashi ya cika da mamakin mai siminti
Mutumin ya mayar masa da ragin da aka samu a kowani buhun siminti Hoto: Abdulrazak Rogo
Asali: Facebook

A cewar Abdulaziz, mai siyar da simintin ya fada masa cewa an rage farashin kowani buhun siminti zuwa N7,800.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saboda haka, sai 'dan kasuwan ya mayarwa abokin cininkin nasa canjin N400 kan kowani buhu sakamakon ragowar da aka samu a farashin kayan.

Ahmad ya bayyana a Facebook.

"A yau na siya buhun siminti kan N8,200, yanzu, mai siyarwan ya kira ni sannan ya ce an rage farashin zuwa N7,800, don haka zai mayar mani da canjin N400 kan kowani buhu.
Idan ba a Arewa ba, ina hakan zai iya faruwa a Najeriya?"

Ga rubutun nasa a kasa:

Martanin jama'a kan farashin siminti

Fatima Mahmud Muhammad ta yi martani:

"Gaskiya yana da amana. Yanda ya tsarkake zuciyar sa da dukiyar sa Allah ya kara buda masa kasuwar sa,Amin."

Kara karanta wannan

Tsadar siminti: Wani mutum ya kara kudin hayar gidansa da ya gina shekaru 30 da suka wuce

Muhammed Ibrahim Sadau ya ce:

"Allah ya saka masa da alheri."

Ahmad Haruna Rimi ya yi martani:

"Allah ya yalwata arzikinsa."

Alawiyyar Alan Waka ya ce:

"Gaskiya irinsa sunyi karanci a cikin Yan kasuwarmu."

Wani mutum ya kara kudin haya saboda siminti

A wani labarin na daban, wani 'dan Najeriya mai gidan haya ya ce dole masu haya a gidansa su kara kudin haya saboda an samu kari a farashin siminti.

An rahoto cewa mutumin ya kara kudin hayar gidansa, yana mai nuni ga tashin farashin kayan gini kamar siminti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng