Kano: Jerin Albishir 5 da Gwamna Abba Ya Yi wa Sheikh Daurawa da Hisbah a Zaman Sulhu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - A ranar Litinin da ta gabata, 4 ga watan Maris, 2024, shugaban Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa da Gwamna Abba Kabir suka sasanta a gidan gwamnatin Kano.
Washe gari ranar Talata, babban kwamandan Hisbah ya koma bakin aiki kuma ya samu tarba mai kyau daga dakarun hukumar da ma mutanen gari masu fatan Alheri.
A jawabin da ya yi bayan isa hedikwatar Hisbah, Malam Aminu Daurawa ya ce mai girma Gwamnan Kano ya yi musu alkawurran inganta ayyukansu da samar musu da kayan aiki.
A faifen bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Daurawa ya lissafa alkawura biyar da mai girma gwamna ya ɗauka a zaman da suka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alƙawrra 5 da Abba ya ɗaukarwa Hisbah
Legit Hausa ta haɗa maku waɗannan alƙawura, ga su kamar haka:
1. Gwamna Abba Yusuf ya yi alƙawarin samar da sabbin motocin aiki ga Operation Kau da Baɗala da kuma inganta shirin 'taya ni mu gyara, wanda Hisbah ta bullo da shi domin kananan ƴara mata.
2. Gwamnatin Abba za ta ƙarawa dakarun rundunar Hisbah albashi wanda bayanai suka nuna tun shekaru 20 da suka wuce N10,000 ake biyansu da N15,000 ga jami'an da ke hedkwata.
3. Za a samar wa hukumar Hisbah isassun kayan aiki.
4. Haka nan kuma gwamnan ya lashi takobin cewa ba za a sake korar jami'an Hisbah saboda siyasa ba.
5. Na ƙarshe shi ne za a kafa makarantar koyar da aikin Hisbah.
Hisbah ta bada dama ga masu son tuba
Babban malamin ya ƙara da cewa Hisbah ta ba duk wani mai aikata baɗala tsawon mako biyu ya tuba, sannan ta buɗe kofa ga duk wanda ya tuba ya kawo kansa.
A cewarsa, zasu ba duk wanda ya tuba fom ya cike wanda za a kaiwa gwamna, "domin ya tallafa masa da jarin sana'a, wanda zai koma makaranta a taimaka masa."
Hisbah: Jerin ayyukan Daurawa a ƙasa da watanni 8
A wani rahoton kuma Shugaban Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ɗauko wasu muhimman ayyukan gyaran tarbiya bayan sake naɗa shi kusan watanni 8 da suka wuce.
Mun tattaro muku muhimman ayyukan alheri da gyaran tarbiya 5 da Daurawa ya aiwatar a tsawon wannan lokaci, cikinsu harda batun auren gata.
Asali: Legit.ng