Jerin Farashin Buhun Simintin Ɗangote, BUA da Wasu Kamfanoni 2 Bayan Ganawa da Gwamnatin Tinubu

Jerin Farashin Buhun Simintin Ɗangote, BUA da Wasu Kamfanoni 2 Bayan Ganawa da Gwamnatin Tinubu

  • Har yanzun farashin siminti na ci gaba da hauhawa a Najeriya duk da yarjejeniyar da FG ta cimma da Ɗangote, BUA da sauran kamfanoni
  • Mun tattaro muku farashin da ake sayar da buhun siminti na Ɗangote da sauransu, an ce yana ƙaruwa ne saboda yawan neman da ake masa
  • A zaman da suka yi da gwamnatin tarayya, masana'antun siminti sun amince za su rage farashin da kusan kashi 50 cikin 100

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Dangote, BUA, Lafarge da sauran manyan masana'antun siminti sun amince za su rage farashin siminti a Najeriya bayan wata ganawa da gwamnatin tarayya.

Taron wanda ministan ayyuka, David Umahi ya shirya, ya samu halartar ministan masana'antu, kasuwanci da zuba jari a Abuja ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu, 2024.

Kara karanta wannan

Shugaban Kwastam ya bayyana a gaban majalisa, ya faɗi gaskiya kan siyar da kayan abinci ga talakawa

Farashin siminti a Najeriya.
Jerin Farashin Simintin Ɗangote, BUA da wasu kamfanoni bayan ganawa da Tinubu Hoto: Dangote Industries, BUA Group
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, gwamnatin tarayya ta kira taron ne sakamakon koken ƴan Najeriya kan hauhawar farashin siminta a faɗin ƙasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan lamari dai ya biyo bayan tashin farashin kayayyakin abinci na amfanin yau da kullum wanda ya jefa ƴan ƙasa cikin wahalhalun tsadar rayuwa.

Alal misali, ana siyar da buhun siminti tsakanin Naira 10,000 zuwa N14,000, ya danganta da simintin na wane kamfani ne.

Rahotanni sun nuna cewa duk da yarjejeniyar da aka yi tsakanin masana’antun da gwamnati na rage farashin da kusan 50%, har yanzu ana sayar da siminti kusan kamar yadda ake sayar da shi kafin taron.

Me ya sa farashin siminti ke hauhawa?

A cewar shugaban kungiyar masu sana’ar siminti ta kasa (CEPAN), David Iweta, farashin siminti na ci gaba da ɗagawa ne sabida neman da ake masa ya fi wanda ake samarwa.

Kara karanta wannan

Ana dab da azumi, tsageru sun shiga babban Masallacin Jumu'a, sun tafka mummunar ɓarna

Ya ce samun kyakkyawar fahimta da gwamnatin tarayya na iya janyo faduwar farashin siminti a cikin kwanaki 30.

Mista Iweta ya kuma zargi tashin farashin dala da taimakawa wajen hauhawar farashin simintin, rahoton The Cable.

Jerin farashin da a ke siyar da siminti a yanzu haka

Kamar yadda binciken baya-bayan nan ya nuna, Legit Hausa ta tattaro muku farashin buhun siminti a Najeriya, ga su kamar haka:

Kamfanin simintifarashin kowane buhu
ƊANGOTEN11,000 zuwa N13,000
BUAN10,000 zuwa N12,000
LAFARGEN13,000 zuwa N14,000
IBETON10,000 zuwa N12,500
UNICEMN11,000 zuwa N13,000

Wakilin Legit Hausa ya zanta da wani dilan siminti a karamar hukumar Ɗanja kan yanayin farashin da suke siyar da kayan a wannan lokacin.

Malam Lawal mai siminti ya shaida mana cewa a yanzu dai suna siyar da kowane buhu ɗaya kan N8,000.

Haka nan wani kwastoma, Shu'aibu Sa'adu ya tabbatar mana da cewa ya siya buhu 3 jiya Laraba kan N8,000, inda ya koka kan tashin farashin da kusan 100%.

Kara karanta wannan

Sauƙi ya zo yayin da Gwamnatin Tinubu za ta fara rabon kayan abinci kyauta a jihohin Najeriya

"Farko lokacin da na fara siyan siminti da zai yi gini ko N4,000 bai kai ba, amma zuwa lokacin da na ɗan tsaya, N4,500 ake diyarwa.
"Abun mamakin jiya da zan ci gaba da aiki wai aka ce mun N8,000, to amma haka nan na siya, muna fatan gwamnati ta shigo lamarin domin ta nan ne za a taimaki talaka."

Shugaba Tinubu ya aike da saƙo ga masana'antun siminti

A wani rahoton na daban kuma Bola Ahmed Tinubu ya umarci kamfanonin da ke samar da siminti su koma asalin farashin siminti na baya kafin faɗuwar Naira

Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce Tinubu ya bai wa kamfanonin wannan umarni ne yayin ganawarsu a makon da ya wuce a Villa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262