An Rasa Rai Yayin da Dakarun Sojoji Suka Gwabza da Ƴan Bindiga, Sun Samu Babbar Nasara a Arewa
- Dakarun sojin Operation Hadarin Daji sun hallaka ɗan bindiga yayin da suka kai ɗauki kauyen Tsohuwar Tasha a ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Zamfara
- Sojojin sun samu nasarar fatattakar ƴan bindigan tare da ceto mutane 15 da maharan suka yi yunkurin yin garkuwa da su
- Babban kwamandan rundunar ya jinjinawa sojoji kana ya roƙi su ci gaba da haka domin tabbatar da zaman lafiya a faɗin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - Sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe wani dan bindiga a yankin ƙauyen Tsohuwar Tasha da ke karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara.
Haka nan kuma dakarun sojojin sun ceto wasu mutane 15 da ‘yan bindigar suka yi yunkurin yin garkuwa da su a ranar Talata, 5 ga Maris, 2024, Channels tv ta rahoto.
Sojojin sun kai ɗauki ne biyo bayan kiran gaggawa da aka yi wa dakarun Operation Hadarin Daji (OPHD), wanda ya tilastawa maharan janyewa ba shiri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Laftanar Suleiman Omale, mai magana da yawun rundunar sojin Operation Hadarin Daji ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Talata.
Sojoji sun ragargaji ƴan bindiga
"Yayin bin sawun ƴan ta'addan, gwarazan dakarunmu suka sheƙe ɗan bindiga ɗaya a hanyarsu ta guduwa, sauran kuma suka arce da raunin harbi.
"Sun kuma ceto mata takwas da maza bakwai daga hannun ƴan bindiga ba tare da sun ji rauni ba. Za mu tabbatar da tsaro a yankin ta hanyar zage dantse wajen sintiri.
"Dakarun sojojin rundunar OPHD za su ci gaba da zama cikin shirin ko ta kwana a kowane lokaci."
- Suleiman Omale.
Manjo Janar GM Mutkut, babban kwamandan runduna ta 8 ta jihar Sakkwato, ya yaba da kwazo da kuma jajircewar da dakarun sojojin suka nuna.
Ya kuma bukace su da su kara dagewa a wannan yaƙi har sai an samu cikakken zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma da kuma fadin Najeriya baki daya.
Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar ‘yan bindiga. Sauran sun hada da Katsina, Sokoto, Kebbi, da Kaduna.
Ƴan bindiga sun yi wa sojoji ɓarna
A wani rahoton na daban Ƴan bindiga sun kai hari kan sojojin Najeriya, sun kashe soja ɗaya tare da mutane da yawa a kananan hukumomi 2 a jihar Benuwai.
Kwamandan rundunar OPWS, Manjo Janar Sunday Igbinomwanhia, ya tabbatar da kashe sojan, amma ya ce dakarun sun halaka yan bindiga uku.
Asali: Legit.ng