Daurawa: Ana Tsaka da Sulhu Tsakanin Abba da Hisbah, Hukumar Ta Samu Babbar Nasara
- Ana tsaka da yin sulhu tsakanin Hisbah da Abba Kabir Yusuf, hukumar ta yi nasarar dakile wata badala a Kano
- Al’ummar Kiristoci da ke unguwar ne suka kai korafi inda suka koka kan yadda aka bude gidan Galan a tsakiyar unguwa
- Hukumar Hisbah ta yi nasarar cafke mata bakwai da maza uku a hanyar Zungeru da ke karamar hukumar Fagge a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Yayin da aka yi sulhu tsakanin gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da Hisbah, hukumar ta yi nasarar cafke wasu a gidan Gala.
Hukumar ta cafke wasu mutane 10 da suke aikata badala a gidan Gala da ke tsakiyar unguwa wanda ya dami jama’a.
Nasarar da Hisbah ta samu a Kano
Wannan kamen na zuwa ne bayan wasu Kiristoci sun kai korafi ga hukumar Hisbah a hanyar Zungeru da ke karamar hukumar Fagge a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aliyu Usman wanda ke kula da bangaren bincike na hukumar ya ce sun samu korafi ne daga al’ummar da ke zaune a yankin, cewar Daily Trust.
“Mazauna unguwar ne suka kawo korafi kan gidan Galan da aka bude a tsakiyar unguwa ta hanyar lauyoyinsu.
“Jami’anmu sun je gidan kuma sun yi nasarar kama mata bakwai da kuma maza uku wanda daya daga cikin mazan bai wuce shekaru 15.”
- Aliyu Usman
Matakin da Hisbah ta dauka kan matasan
Usman ya kara da cewa tuni suka tura su kotu domin ta dauki matakin da ya ce a kan wadanda ake zargin.
Ya ce barin kananan yara irin wadannan zuwa gidajen badala babbar masifa ce kuma zai kawo cikas a kokarin gyaran da ake yi.
Wannan ya biyo bayan dawowar shugaban hukumar, Sheikh Daurawa kan kujerarsa a jiya Litinin 4 ga watan Maris, cewar Premium Times.
Daurawa da Hisbah sun ba ‘yan iska wa’adi a Kano
Kun ji cewa shugaban hukumar Hisbah ya bai wa masu yada badala wa’adin kwanaki 14 da su tuba ko su bar jihar.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana haka jim kadan bayan yin sulhu da Gwamna Abba Kabir a gidan gwamnatin jihar.
Wannan na zuwa ne bayan Daurawa ya yi murabus daga kujerar kan wasu maganganu da Gwamna Abba ya yi.
Asali: Legit.ng