Hotuna Sun Bayyana Yayin da Malamin Addini Ya Raba Kayan Abinci Kyauta Ga Mabiyansa

Hotuna Sun Bayyana Yayin da Malamin Addini Ya Raba Kayan Abinci Kyauta Ga Mabiyansa

  • Soshiyal midiya ta cika da kalaman yabo kan yunkurin wani Fasto na rage raɗaɗin da mutane ke ciki na tsadar rayuwa da yunwa
  • Bayan kammala ibada ranar Lahadi a birnin Uyo, malamin ya rabawa mutane buhunan shinkafa da doya domin rage raɗaɗi
  • Da yawan masu amfani da kafafen sada zumunta sun yaba wa wannan mataki da cewa ya kamata ya zama abin koyo ga sauran coci-coci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Bayan kammala ibada, wani Fasto na cocin Dunamis International Church a Uyo ya rabawa mabiyansa tallafin kayan abinci domin rage masu raɗaɗi.

Malamin addinin ya rabawa mabiyansa masu zuwa ibada a cocin kayan abinci da suka haɗa da shinkafa, doya da sauran kayan amfani na yau da kullum.

Kara karanta wannan

Sauƙi ya zo yayin da Gwamnatin Tinubu za ta fara rabon kayan abinci kyauta a jihohin Najeriya

Fasto ya raba kayan abinci kyauta ga mabiyan cocinsa.
Malamin coci ya raba abinci a coci a Uyo Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

Wannan jin ƙai na zuwa ne yayin da ƴan Najeriya ke fama da wahalhalun rayuwa da tsadar kayayyaki tun bayan kama aikin sabuwar gwamnati a watan Mayu, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin dai ya kai ga mutane suna daka wawa kan motocin abinci kuma a kwanan nan aka wawushe abinci a wani rumbun ajiya a Abuja.

Malamin ya saba taimakawa al'umma

Dama dai tun kafin haka, alherin wannan fasto ba ya ɓoyuwa domin ya saba tallafawa ɗalibai da ke buƙatar taimako a harkokin karatunsu, The Nation ta ruwaito.

Waɗanda suka ci gajiyar wannan tallafin sun nuna farin ciki da godiya, inda suka bayyana yadda cocin ke taka rawa wajen walwalar mabiya musamman a lokacin matsin tattalin arziƙi.

Yayin da sauran malaman coci suka dakatar da tattara kuɗi daga mabiya, Faston cocin Dunami ya ɗauki matakin tallafi kai tsaye domin agazawa mabuƙata.

Kara karanta wannan

Boko Haram: Sama da 90% na ainihin masu aƙidar ta'addanci sun mutu Inji Zulum

Wannan aiki da malamin ya yi ya jawo masa yabo a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka yi fatan ya ɗore a haka.

Ƴan Najeriya sun yi martani

Wasu daga cikin martanin da mutane suka yi yayin da Vanguard ta wallafa labarin sun ƙunshi:

Kenny Samuel Ogoina ya ce:

"Abun al'ajabi kenan yadda soyayya take komawa ga mutane, Allah ya ƙara taimakonka yallabai."

Ifeanyi Ezemenari ya ce:

"Wannan ba ƙaramin ci gaba bane, abin da ya kamata sauram coci-coci su koya a matsayin ɓangaren kula da walwalar mabiyansu. Allah ya albarkaci Dunamis."

Daniel Awka ya ce:

"Abin mamaki, mai kyau, haziƙin aiki, amma kamata ya yi a yi rabon abincin a wajen coci, ba a cikin wuri mai tsarki ba; Allah ya albarkace ka, fasto, saboda irin kulawar da ka nuna."

Ina aka kwana a batun raba hatsin FG?

A wani rahoton mun kawo muku cewa a wannan makon za a fara rabon hatsi tan 42,000 a faɗin jihohi 36 a Najeriya.

Ministan noma da samar da isasshen abinci, Abubakar Kyari, ya ce za a bi matakan da suka dace wajen tabbatar da tallafin ya isa ga talakawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262