Daurawa Ya Dawo da Karfinsa, Ya Ba 'Yan Daudu da Matan Banza Wa'adin Kwana 14 a Kano

Daurawa Ya Dawo da Karfinsa, Ya Ba 'Yan Daudu da Matan Banza Wa'adin Kwana 14 a Kano

  • Shugaban hukumar Hisbah ta Kano, Sheikh Aminu Daurawa, ya aika muhimmin sako ga masu aikata badala a jihar jim kadan bayan dawowarsa kujerarsa
  • Daurawa ya gargadi 'yan daudu da karuwai a Kano da su tuba ko su tattara kayansu sun fice daga jihar cikin makonni biyu masu zuwa
  • Shehin malamin ya kuma bayyana tanadin da suka yi wa duk wadanda suka tuba ta hanyar yankar wani fam mai taken 'Na tuba' a ofishin Hisbah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Kano - A ranar Litinin, 4 ga watan Maris ne labarin komawar Sheikh Aminu Daurawa kan kujerarsa ta shugabancin Hisbah ya bayyana.

Tun farko dai Daurawa ya yi murabus daga kujerarsa ne bayan sukar wasu daga cikin ayyukan 'yan Hisbah da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane matsorata ne, sun cancanci hukuncin kisa, Remi Tinubu ta magantu a bidiyo

Bayan ban hakuri da zaman sulhu, an cimma matsaya inda Shehin malamin ya koma bakin aikinsa.

Daurawa ya aika sako ga 'yan daudu da karuwai a Kano
Daurawa ya ba 'yan daudu da karuwai wa'adin barin Kano Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, yayin da wasu ke ganin abubuwan da suka faru a baya za su kawo cikas ga ayyukan Hisbah, Shehin malamin ya ce hakan karfafa masu gwiwar kara kaimi kan ayyukansu ya yi.

Mun ba ku makonni biyu ku tuba - Daurawa ga masu badala

Daurawa ya kuma ce sun ba duk wasu masu yada badala, kama daga 'yan daudu zuwa mata masu zaman kansu makonni biyu su tuba, sannan cewa za a basu kudi domin su ja jari tare da koya masu sana'a.

A wata hira da aka yi da shi, malamin ya gargadi wadanda ba su da niyyar tuba da su tattara su bar Kano domin jihar ba ta fasikai bace.

Kara karanta wannan

Kiran juyin mulki: Minista ya dauki zafi, ya bada umarni ga jami'an tsaro a dauki mataki

Hirar da aka yi da Daurawa bayan dawowa Hisbah

A hirarsa da sashin Hausa na BBC, malamin ya ce:

“Yanzu ai kara karfafawa aka yi, yanzu babu wani takunkumi, dari bisa dari babu wani sharadi da aka yi cewa za mu mayar da aikinmu baya face ma an ce za a karfafa mana gwiwa ne don aiki ya ci gaba fiye da da.
“Don haka ne yanzu wani abu da ya faru kamar ma ya bazawa abin taki ne, don haka wadanda suke ganin ‘yan daudu ne da karuwai da fasikai hukumar Hisbah ta basu sati biyu wanda yake so zai tuba.
"Akwai fam da muka buga sunansa na tuba za a ba mutum ya je ya cika, za a ba mutum jari, za a koya masa sana’a, za a mayar da shi garinsu idan ba ‘dan Kano ba ne.
“Wanda kuma bai tuba ba, ba kuma zai bi dokoki ba zai ci gaba da karya doka toh lallai gara ya tattara kayansa ya kara gaba, Kano ba matattarar badala bace."

Kara karanta wannan

Kano: Jerin albishir 5 da Gwamna Abba ya yi wa Sheikh Daurawa da Hisbah a zaman sulhu

- Aminu Daurawa

Wata 'yar Kano ta nuna karfin gwiwa a ayyukan 'yan Hisbah sannan ta goyi bayan fatattakar 'yan iska daga Kano dari bisa dari.

Zainab Ummi ta ce:

"Gaskiya muna tare da ayyukan 'yan Hisbah a jiharmu, wai ace Kano ta zama matattara ta karuwai da 'yan daudu da duk wasu masu aikata masha'a. Ta yaya kuwa bala'i ba za su dunga saukar mana ba.
"Muna tare da Sheikh Daurawa a aikin da yake na tsaftace jiharmu daga 'yan iska da masu aikata badala. A kori duk wasu 'yan iska su koma jiharsu, don yawanci dama ba 'yan gari bane, baki ne da ke shigo mana.
"Duk wanda bai ajiye makamin iskanci ba toh ya kamata ya 'dandana kudarsa."

Sheikh Daurawa ya magantu kan komawa Hisbah

A baya mun ji cewa shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa ya tabbatar da komawarsa kan kujerarsa bayan ya sanar da yin murabus a baya.

Daurawa ya tabbatarwa sashin Hausa na BBC cewa hukumar Hisbah za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na kawar da badala da tabbatar da tarbiya kamar yadda ta saba a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng