Sufeta Janar Ya Hana Aiki da Na’urar POS a Ofisoshin ’Yan Sanda, Ya Fadi Dalili
- Sufeta Janar Kayode Egbetokun, ya haramta amfani da na’urar POS a ofisoshin ‘yan sanda da dukkan cibiyoyin rundunar da ke a fadin kasar
- Egbetokun ya bayar da wannan umarni ne biyo bayan zargin wasu 'yan sanda na amfani da na'urar POS wajen aikata laifuffuka na kudi
- Olumuyiwa Adejobi, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da fadin abin da ja jawo hakan
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja- Kayode Egbetokun, Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IGP), ya haramta amfani da na’urar hada-hadar kudi ta POS “a cikin harabar ofisoshin ‘yan sanda da cibiyoyinta” a fadin kasar nan.
Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ne ya sanar da dakatarwar a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, 4 ga Maris.
Me yasa IGP ya haramta amfani da POS a ofisoshin ‘yan sanda?
Adejobi ya ce umarnin ya hada da “sauran na’urorin hada-hadar kudi na tafi da gidanka.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin rundunar ya kara da cewa an ba da umarnin ne sakamakon korafe-korafen da jama’a suka yi kan yadda wasu jami’an ‘yan sanda ke hada baki da masu POS ana zaluntarsu.
Kamar yadda BusinessDay ta ruwaito, Adejobi ya kuma ce manufar haramcin shi ne "dakile ayyukan cin hanci da rashawa" da kuma "tabbatar da da'ar jami'an rundunar".
"Don haka, IGP ya yi gargadin cewa za a dauki mummunan mataki kan shugabannin ofisoshin rundunar da aka kama an karya wannan doka."
-A cewar Adejobi
Yan sanda sun kama malamin jami'ar Yobe
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito yadda wani malamin jami'ar kimiya ta jihar Yobe, Mista Adamu Garba Hudu ya shiga komar 'yan sanda a Potiskum, jihar Yobe.
An kama Hudu ne bisa zargin laifin yin lalata da dalibai mata na jami'ar domin ba su maki a darasin da yake koyar da su.
Rundunar ta kama malamin ne bayan gama lalata da wata dalibai a ofishinsa da ke a babban asibitin Potiskum, inda aka gano ya yi lalata da akalla dalibai hudu.
Asali: Legit.ng