Hisbah: Sheikh Daurawa da Malaman Kano Sun Isa Gidan Gwamnati, Sun Sa Labule da Abba

Hisbah: Sheikh Daurawa da Malaman Kano Sun Isa Gidan Gwamnati, Sun Sa Labule da Abba

  • Manyan malaman Kano kaƙashin jagorancin Sheikh Abdulwahab Abdallah sun isa fadar gwamnatin jihar domin ganawa da Gwamna
  • Sheikh Aminu Daurawa na cikin tawagar malaman da suka je gidan gwamnatin da daren ranar Litinin, 4 ga watan Maris, 2024
  • Wannan zama na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan Daurawa ya yi murabus daga kujerar babban kwamandan rundunar Hisbah

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum.

Jihar Kano - Tawagar manyan malumman jihar Kano a karkashin jagorancin Sheikh Abdulwahab Abdallah, sun isa fadar gwamnatin jihar da daren yau Litinin.

Tawagar malaman wanda ta ƙunshi babban kwamandan hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa, ta kai ziyara gidan gwamnatin ne domin ganawa da Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Malaman Kano sun gana da Gwamna Abba.
Amini Daurawa da Malaman Kano tare da Abba Kabir Yusuf Hoto: @baba (Kwankwason Tuwita)
Asali: Twitter

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da shafin Kwankwaso Tuwita ya wallafa a manhajar X watau Twitter yau Litinin, 4 ga watan Maris, 2024.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya sasanta da Aminu Daurawa, ya koma kwamandan Hisbah gadan-gadan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Tawagar Malaman jihar Kano bisa jagorancin Sheikh Abdulwahab Abdallah, tare da babban Kwamandan Hisbah Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, sun iso fadar gwamnatin jihar Kano.
"Za su yi zama na musamman tare da mai girma gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf."

Jerin malaman da ke tare da Daurawa

Malaman da suka halarci zaman sulhun sun haɗa da Sheikh Abdulwahab Abɗallah, Farfesa Musa Barodo, Farfesa Salisu Shehu, Farfesa Sa'idu Dukawa da Dakta Muazzam Khalid.

Sauran waɗanda suka je taron su ne Injiniya Bashir Hanan, Sheikh Shehu Mai Hula, da dai sauransu.

Ana sa ran bayan wannan taro, Sheikh Aminu Daurawa zai haƙura ya koma kan muƙaminsa na shugaban hukumar Hisbah.

Sheikh Daurawa dai ya yi murabus ne bayan Gwamna Abba ya kwance wa Hisbah zani a kasuwa, lamarin da ya jawo cece kuce mai zafi a ciki da wajen Kano.

Kara karanta wannan

Hajj 2024: Gwamna Fintiri ya nada sabon Amirul Hajj na jihar Adamawa, an samu karin bayani

Malamai da dama sun nuna cewa bai kamata gwamnan ya yi waɗannan maganganu a fili ba, yayin da suka nemi ya bai wa Malam Daurawa haƙuri.

Ƴan daudu sun yi barna a hedkwatar Hisbah

A wani rahoton kuma 'Yan daudu sun taru sun kai hari ofishin hukumar Hisbah da ke unguwar Bachirawa karshen kwalta a jihar Kano.

Tsagerun sun farfasa motar 'yan Hisbar tare da basu umurnin sako 'yan uwansu da ke tsare a hannunsu hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262