Mutane 12 Sun Mutu Yayin da Wasu Sama da 20 Suka Ji Raunuka a Babban Titin Zaria Zuwa Kaduna

Mutane 12 Sun Mutu Yayin da Wasu Sama da 20 Suka Ji Raunuka a Babban Titin Zaria Zuwa Kaduna

  • Haɗarin mota ya yi sanadin mutuwar mutane 12 yayin da wasu 28 suka ji raunuka daban-daban a kan babban titin Zariya zuwa Kano
  • Hukumar kiyaye haɗurra ta jihar Kaduna (FRSC) ta ce tsere da gudun da ya wuce ƙima ne suka haddasa faruwar lamarin da safiyar Litinin
  • Kwamandan hukumar, Kabir Y Nadabo, ya ce yanzu haka an kwantar da waɗanda suka ji raunuka a babban asibitin Maƙarfi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - An rasa rayukan mutane 12 ciki har da direban mota yayin da wasu 28 suka ji raunuka a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a kan babban titin Zaria zuwa Kano.

Kara karanta wannan

Boko Haram: Sama da 90% na ainihin masu aƙidar ta'addanci sun mutu Inji Zulum

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro, haɗarin ya faru ne da wata mota mai lambar rijista KTG 454 ZZ a daidai garin Tashar Yari ranar Litinin da ƙarfe 7:36 na safe.

Hadari ya ci mutum 12.
Mutane 12 Sun Mutu Yayin da Wasu Sama da 20 Suka Ji Raunuka a Babban Titin Zaria Zuwa Kaduna Hoto: Federal Road Safety Corps Nigeria
Asali: Facebook

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar haɗarin, wanda ta ce ya faru ne saboda tsere, gudu da kuma lodin da ya wuce ƙima.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadarin mota: Wane hali mutanen da suka ji rauni ke ciki?

Rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka an kwantar da waɗanɗa suka samu raunuka a babban asibitin Maƙarfi domin kula da lafiyarsu.

FRSC ta kuma gayyaci mai motar da haɗarin ya rutsa da ita wanda yake ɗan garin Azare a jihar Bauchi, ya kai kansa hedikwatar hukumar ta jihar Kaduna.

"Tirelar mai lamba KTG 454 ZZ tana kan hanyar zuwa Kano lokacin da lamarin ya faru,” inji hukumar FRSC.

Kara karanta wannan

Dattawa sun tsoma baki kan batun sojoji su kifar da Gwamnatin Shugaba Tinubu kan abu 2

Shugaban ƙaramar hukumar Makarfi da kwamandan hukumar kiyaye haɗurra na sashen Tashar Yari sun je wurin domin tantance asarar da haɗarin ya jawo.

Ta ya za a kawo karshen haɗurran mota a Najeriya?

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, kwamandan FRSC na jihar Kaduna, Kabir Y Nadabo, ya buƙaci masu ababen hawa su riƙa bin dokar tuƙi domin su sauka lafiya musamman a manyan tituna.

Ya ce jami'ansa za su ci gaba da aiki tuƙuru tare da haɗa kai da masu ruwa da tsaki a ɓangaren sufuri domin tabbatar da aminci a kan tituna, The Nation ta ruwaito.

Mutum tara sun mutu a titin Legas-Abeokuta

A wani rahoton kuma kun ji cewa an samu aukuwar wani mummunan hatsarin mota a kan titin hanyar Legas zuwa Abeokuta a ranar Talata, 20 ga watan Fabrairu

Hatsarin motan wanda ya ritsa da mutum 17 ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutum tara yayin da wasu mutum bakwai suka jikkata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262