Halin Kunci: Hukumar Kwastam Za Ta Sake Rabon Kayan Abinci Karo Na 2 Bisa Sharuda
- Yayin da ake cikin wani hali na matsin rayuwa a Najeriya, Hukumar Kwastam za ta sake raba shinkafa a karo na biyu
- Hukumar ta ce Gwamnati ta ba da damar sake rabon shinkafar da aka kwace a hannun jama'a da suke kokarin fitar da ita ba bisa ka'ida ba
- Za a fara rabon kayan abincin ne a shiyyar Oyo da kuma Ogun domin rage musu radadin tsadar abinci da ake fama da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - Hukumar Kwastam a Najeriya ta shirya tsaf domin sake raba kayan abinci da ta kwace domin rabawa marasa ƙarfi.
Hukumar da ke shiyyar jihohin Oyo da Ogun ta ce za ta fara rabon ne da zarar Gwamnatin Tarayya ta tsara yadda za a raba kayan.
Wane mataki Kwastam ta dauka don dakile yunwa?
Wannan na zuwa ne yayin da al'umma ke cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa musamman kayan abinci a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ta ce daukar matakin ya zama dole domin dakile abin da ya faru a jihar Legas yayin rabon, kamar yadda Vanguard ta tattaro.
Abincin da hukumar ke rabawa na daga cikin wanda ta kwace inda ta ke zargin ana ƙoƙarin fitar da shi ba bisa ka'ida ba.
Wane martanin kwamandan Kwatsam ya yi?
Kwamandan shiyyar, Ben Oramalugo shi ya bayyana haka a Ibadan a jiya Lahadi 3 ga watan Maris, cewar Tori News.
Ben ya ce ganin yadda ake cikin wani halin a kasar, Gwamnatin Tarayya ta umarci hukumar Kwastam sake raba kayan da ta kwace.
Jami'in ya ce hakan zai taimaka wurin rage tsadar da ake ciki ganin yadda za a siyar da shinkafar cikin farashi mai rahusa.
Tinubu ya tsayar da ranar raba kayan abinci
A baya, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranar fara rabon hatsi tan dubu 42 yayin da ake cikin tsadar rayuwa.
Gwamnatin ta ce za ta fara rabon kayan ne a mako mai zuwa inda za a fara da jihar Neja da ke Arewacin Najeriya.
Ministan Albarkatun Noma, Abubakar Kyari shi ya tabbatar da haka inda ya ce tallafin zai taimaka wurin rage tsadar abincin.
Asali: Legit.ng