Gwamnan Kano Ya Tura a Yi Bikon Sheikh Aminu Daurawa Ya Dawo Shugabancin Hisbah
- Kwanaki bayan da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi murabus daga shugabancin Hisbah, ana kokarin dawo dashi bakin aiki
- An tura malamai domin shawo kan malamin da ya samu sabani da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf
- Ana zargin hukumar Hisbah da take hakkin mata a lokutan da take kame a yankuna daban-daban na jihar
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Jihar Kano - Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, akwai yiwuwar gwamnatin jihar Kano ta yi bikon Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa don ci gaba da rike hukumar Hisbah.
Wannan kuwa zai faru ne yayin da aka ce gwamnatin tuni ta fara shirye-shiryen bikon malamin tun bayan da ya sanar da yin murabus dinsa daga shugabancin hukumar.
A baya, a Legit ta kawo maku rahoton yadda Daurawa ya yi murabus, inda ya fito a bidiyo ya bayyana matsayarsa game da shugabancin hukumar ta Hisbah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tura malamai bikon Daurawa
A dalilin haka ne ma gwamnatin jihar ta Kano ta tura tawagar malamai a jihar don ganawa da Daurawa tare da rokonsa ya dawo kan kujerarsa.
A rahoton da muka samo daga Aminiya, shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Jibril Falgore da babban limamin masallacin kasa Sheikh Ibrahim Makari na daga tawagar da je bikon malam.
Ya aka yi Daurawa ya bar shugabancin Hisbah?
A bidiyon da ya fitar, Daurawa ya bar shugabancin Hisbah ne biyo bayan martanin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kan yadda hukumar Hisbah ke tafiyar da aikinta.
Kalaman gwamnan dai sun jawo cece-kuce, lamarin da yasa Daurawa ya ajiye aiki sa’o’i 24 bayan danbarwar.
Ana dai ci gaba da bayyana korafe-korafe kan yadda hukumar Hisbah ke yin kame a jihar Kano, inda ake zarginta da take hakkin mata.
Gwamnan Kano ya sace gwiwar Daurawa
A baya, kun ji yadda Sheikh Daurawa ya ajiye aikinsa a hukumar Hisbah biyo bayan kamalan gwamna Abba Kabir Yusuf.
Wannan na zuwa ne bayan da gwamna Abba ya yi tsokaci kan kadan daga ayyukan da hukumar ta Hisbah ke yi.
Wannan lamari dai ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin Daurawa, wasu kuma ke daura laifin ga Abba Gida-Gida.
Asali: Legit.ng