Tsadar Rayuwa: Tun da Muka Tsallake Ƙangin Mulkin Buhari a 1984, Wannan Ma Zai Wuce, Malamin Addini

Tsadar Rayuwa: Tun da Muka Tsallake Ƙangin Mulkin Buhari a 1984, Wannan Ma Zai Wuce, Malamin Addini

  • Yayin da ake cikin mawuyacin hali a Najeriya, malaman addini na ci gaba da kwantar wa jama’a hankali tare da rokon karin hakuri
  • Wannan karo Fasto Henry Ojo ne ya yi wannan roko inda ya ce idan har za a tsallake mulkin Buhari na farko to wannan mai sauki ne shi ma zai wuce
  • Faston ya bayyana haka ne ga ‘yan jaridu bayan kaddamar da sabon cocin Christ Apostolic a ranar Asabar 2 ga watan Maris a jihar Oyo

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Babban Fasto a Najeriya, Dakta Henry Ojo ya roki ‘yan kasar da su kara hakuri kan halin da ake ciki na kuncin rayuwa.

Kara karanta wannan

Bayan Dangote, jama'a sun tare motar BUA, an wawushe kayan abinci ana tsakiyar yunwa

Malamin wanda shi ne shugaban cocin Christ Apostolic gida da waje ya ce wannan yanayi ba bako ba ne a Najeriya, cewar Tribune.

Malamin ya fadi irin jarabawar da suka tsallake a mulkin Buhari na farko
Fasto Henry ya ce tun da suka tsallake tarkon Buhari a 1984 komai zai wuce. Hoto: Muhammadu Buhari, Henry Ojo.
Asali: Facebook

Menene Faston ke cewa kan mulkin Buhari?

Faston ya bayyana haka ne ga ‘yan jaridu bayan kaddamar da sabon cocin Christ Apostolic a ranar Asabar 2 ga watan Maris, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Henry ya ce a baya ma lokacin mulkin Buhari na farko a shekarar 1984 an fuskanci fiye da haka kuma an tsira.

A cewarsa:

“Tun da ubangiji ya sa muka tsallake wancan jarrabawar yanzu ma za mu tsallake wannan halin da ake ciki."

Ya ba da tabbacin samun sauki a kasar

Ya kara da cewa:

“Dole mu yi hakuri da wannan gwamnati, abin da muke fama da shi ba bakon abu ba ne a tarihin wannan kasa.

Kara karanta wannan

Dangi sun shiga makoki yayin da tuwo ya kashe mutum, aka kwantar da 4 a asibiti

“Mun fuskanci babbar matsalar halin kunci lokacin mulkin Buhari a 1984 ba mu manta ba amma kuma mun tsallake wancan lokaci.”

Ya ce tun da ‘yan Najeriya suka tsallake jarabawar wancan lokaci yanzu ma za a tsallake ba tare da wata matsala ba.

Fasto Mustapha ya roki ‘yan Najeriya

Kun ji cewa wani fitaccen Fasto a Najeriya, Solomon Mustapha ya roki ‘yan Najeriya karin hakuri kan halin da ake ciki.

Faston ya ce wannan hali da ake ciki na wucin gadi ne kuma mai wucewa ne ba tare da bata lokaci ba.

Malamin ya bayyana haka ne a dai-dai lokacin da ake fama da tsadar kayayyaki musamman na abinci a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.