Matashiyar Lauya Ta Ajiye Satifiket Dinta, Ta Zama Mai Siyar da Koko
- Wata ‘yar Najeriya ta bayyana sabon aikin da ta kama na siyar da koko bayan ta shafe shekaru 5 a jami’a
- Matar wacce ta yi karatun lauya a jami'a ta bayyana cewa bata taba samun damar aiki da abin da ta karanta ba tsawon shekaru
- Masu amfani da soshiyal midiya sun garzaya sashin sharhi don yin martani ga wallafar da ta yi inda da dama suka jinjinawa kwazonta
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Wata ‘yar Najeriya wacce ta shafe tsawon shekaru biyar tana karatun lauya a jami’a ta yi watsi da satifiket dinta don zama mai siyar da koko.
Matar mai suna @pasieynaturalfoods a TikTok ta yi ikirarin cewa ita ke siyar da koko mafi amfani a jiki.
Lauya ta zama mai siyar da koko bayan kammala karatu
Wani hoto da ta wallafa a shafinta ya nuno ta sanye da kayan lauyoyi bayan ta kammala karatunta na digiri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da bidiyon ya ci gaba, an gano sauyi a aikinta yayin da take ta hada sinadaren yin koko.
Cike da alfahari mai kokon ta kuma wallafa bidiyonta tana nika sinadaren koko ciki harda ayaba, karas, dabino, da sauran kayan marmari masu amfani.
Ta yiwa bidiyon take da:
“Ni ke hada koko mafi amfani a jiki a duk fadin Najeriya.”
Jama'a sun yi martani
@user2369219617738 ya ce:
“Nima ina so na karanci fannin lauya don Allah imna iya ci gaba?"
Mummy_Tee ta ce:
“Gani nan takwara ta, nima na shiga sana’ar abinci yanzu.”
Midey ta yi martani:
“Najeriya ta gaza mana sannan ina son mutanen wannan zamani, Allah ya kawo ciniki maama, nima ina gasa cincin mai dadi.”
Yadda ma'aikaciyar banki ta ajiye aikinta na shekaru 13, ta kama sana'ar da ke kawo mata kudi kullun
@iamSplendid ta ce:
“Waow Allah ya albarkaci kwazonki ta yaya kika koyi yadda ake nika?”
Hidah rta yi martani:
“Babban abun shi ne kina iya yiwa kanki komai, Allah ya bunkasa kasuwancinki.”
Ma'aikaciyar banki ta zama mai kiwo
A wani labarin, mun ji cewa wata mata 'yar Najeriya wacce ta bar aiki a matsayin ma'aikaciyar banki ta rungumi noma ta ja hankalin mutane da dama da labarinta.
Wani 'dan gajeren bidiyo na sana'ar kiwon da take yi ya yi bayanin cewa ta mayar da gidanta ya zama wajen da take kiwon kifi da kaji lokacin annobar Korona, wanda ya yi sanadiyar yi wa mutane kulle.
Asali: Legit.ng