Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Birnin Tarayya, Sun Sace Mutane da Dama
- Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindiga da yawan su ya zarce 40 sun kai sabon farmaki karamar hukumar Bwari da ke FCT, Abuja
- Sun kai farmakin ne gundumar Kawu, inda suka yi awon gaba da tsohon shugaban jam'iyyar PDP na gundumar tare da yaransa hudu
- Haka kuma sun yi awon gaba da amaryar mai gundumar garin tare da yaronsa Lukman, sun kuma sace sarkin pawa da matansa da yara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
FCT, Abuja - Yan bindiga sun kai sabon farmaki gundumar Kawu da ke karamar hukumar Bwari da ke babban birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis.
A yayin harin, sun yi awon gaba da tsohon shugaban jam'iyyar PDP na gundumar, Alhaji Alhassan Sidi Kawu da ƴayansa hudu da wasu mutane 18.
Shugaban karamar hukumar Bwari, Abdulmumini Zakari, ya shaidawa manema labarai cewa ƴan bindigar sun dira gundumar ne a ranar Laraba daga dajin Kuyeri da ke Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa akwai mata da yaron mai gundumar yankin, Alhaji Abdulrahman Danjuma Ali a cikin wadanda aka sace, rahoton The Punch.
Yadda ƴan bindigar suka kai farmakin
Zakari ya ce:
"Sun raba kansu ne gida gida, wasu suka tafi gidan mai sarautar gudnumar, Alhaji Abdulrahman, inda suka sace amaryarsa da yaronsa Lukman.
"Wasu kuma sun farmaki gidan Alhaji Alhassan Sidi Kawu, Marafan Kawu kuma tsohon shugaban PDP na gundumar, sun tafi da shi da yaransa hudu."
Yan sanda ba su ce uffan kan harin ba
Haka kuma an ruwaito cewa ƴan bindigar sun farmaki gidan Sarkin Pawan Kawu, Gambo Pawa, wanda suka sace shi tare da matansa biyu da yara.
Duk wani yunkuri na manema labarai na jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan Abuja, SP Josephine Adeh ya ci tura.
Kudin tsafi: An kama matashin da ya kashe ƴan mata
A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta kama Adebayo Olamide Azeez, matashin da ya kashe ƴan mata bakwai don a biya shi kudi da nufin yin tsafi da sassan jikin su.
Azeez wanda ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, ya bayyana cewa ana biyan sa naira dubu 30 zuwa naira dubu 40 idan ya kashe mace ɗaya.
Ya kuma bayyana cewa yana amfani da wata manhajar soyayya ce mai suna MyChat wajen haduwa da ƴan matan, wadanda yake yaudarar su da sunan zai biya su kudi don su yi fasikanci.
Asali: Legit.ng