Karayar Arziki: Kamfanin Nestlé Ya Fada Cikin Mawuyacin Hali Bayan Faɗuwar Naira
- Babban kamfanin sarrafa kayayyakin abinci, Nestle Nigeria ya tafka asarar biliyoyin naira bayan da darajar Naira ta fadi a kasuwar duniya
- Nestle ya fitar da wani binciken asusunsa a ranar Laraba, wanda ya nuna bashin da ake binsa na naira biliyan 115.3 ya koma naira biliyan 402.3
- Biyo bayan matsin tattalin da faduwar Nairar ta haifar, kamfanonin kasashen duniya ciki har da Procter & Gamble da GSK na ta ficewa daga kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kamfanin Nestlé Nigeria ya bayar da rahoton cewa, kudaden bashin da ke kansa a shekarar d2023 sun zarta darajar kadarorinsa da naira biliyan 78.1, bayan faduwar darajar Naira.
Wannan lamari ya jefa kamfanin cikin asarar makudan kudaden, kamar yadda binciken kudaden asusun kamfani ya nuna a ranar Laraba.
Jimlar kudin bashin na shekarar 2023 ya karu zuwa naira biliyan 659.8 daga Naira biliyan 384.8 a shekarar bara sakamakon karuwar asarar kudaden waje, rahoton Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanoni sun fara gudun Najeriya
Haka dai shi ma kamfanin PZ Cussons Nigeria ya bayyana irin wannan asarar a makon da ya gabata, inda ya ce darajar dukiyarsa ta ragu da naira biliyan 23.2.
Biyo bayan matsin tattalin da faduwar Nairar ta haifar, kamfanonin kasashen duniya ciki har da Procter & Gamble da GSK na ta ficewa daga kasar.
Lamunin da ya karba a dalar Amurka ya mamaye sama da kashi 60 cikin 100 na kadarorin Nestlé Nigeria, a cikin shekarar da Naira ta fadi warwas.
Nestle Nigeria, reshe ne na Nestle S.A na Switzerland
Channels TV ta ruwaito cewa bashin da ake bin katafaren kamfanin kayan masarufin ya haura zuwa naira biliyan 402.3 daga naira biliyan 155.3 a cikin shekara guda.
Nestle Nigeria, reshe ne na babban kamfanin abinci na duniya Nestle S.A. na Switzerland, kuma ya sami hanyar shiga kasar ne shekara daya bayan samun 'yancin kai a 1961.
Ya kasance babban kamfanin samar da kayan masarufi tare da manyan kayayyaki irin su Milo, Nescafe, Golden Morn, Maggi da sauransu.
Manyan kamfanoni 3 sun tafka asarar naira biliyan 140
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa akwai wasu kamfanoni uku da suka tafka asarar naira biliyan 140 sakamakon karyewar darajar Naira a kasuwar hada-hadar kudi ta duniya.
Kamfanoni irin su BUA, Flourmills, Cadbury da wasu bankuna sun fuskanci barazanar asarar kudi daga hauhawar farashin dala a kasuwa.
Asali: Legit.ng